Wadannan dabi’u abin yabo kuma masu kyawu, suna da yawa amma za mu maida hankali kan asalinsu ko kuma mu ce tushensu, don tabbatar wa halittu cewa dukkkansu, Annabi SAW ya dabi’antu kuma ya hakikantu da su.
Asalin reshen wadannan kyawawan dabi’un shi ne ‘Hankali’. Hankali shi ne komai, in za a fara gyaran dabi’un Dan’adam, hankalinshi ake fara hukunci da shi, in babu hankali, hukuncin shari’a ya fadi a kanshi. Daga hankali, ilimi ke tasowa da sanin Allah ta hanyar amfani da “Aklul a’ala”.
- A Shirye Kasar Sin Take Ta Kyautata Dangantakar Tattalin Arziki Da Amurka
- Dole Mu Bai Wa Matasan Nijeriya Dama A 2027 – Bafarawa
Don haka, dole Dan’adam ya kiyaye hankalinsa, sabida komai na alkhairi ta hankali yake tasowa. Ja’afaru dan Abi Dalibi an ruwaito cewa ko a lokacin Jahiliyya bai taba shan giya ba, an tambaye shi me ya sa? Ya ce “Abin da zai dada min hankali nake so ba wanda zai rage min ba.
Kowa yana da hankali sai dai na wani ya fi na wani, wani yana da kaifin hangen nesa, in ya kawo ra’ayi yana tabbata, saba masa a kan ra’ayin kan sa a samu kuskure. Mai hankali ya fi kowa kyawun tsari da tafiyar da al’amura ta irin yadda suka dace. In ma’anar hankali shi ne komai kuma wanda ya fi hankali ya fi kowa iya tsarin rayuwa da jagorantar al’umma, in haka ne, Annabi (SAW) ya fi kowa ‘hankali’. Manzon Allah (SAW) ya kai matuka a cikin hankali da Ilimi wanda babu wani Dan’adam da ya yi kusa da shi sabida shi ‘Sayyadil Bashari’ ne mai ‘Aklul a’ala’ kuma shi ke da jawami’il kalimi – In ya fadi magana daya amma a yi mata ma’anoni daban-daban. Allah ya bashi Ilimin da ke cikin Attaura da Injila da duk littattafan da Allah ya saukar wa Annabawansa kafin zuwa Annabi (SAW). Allah ya ba shi Hikimar masu hikima, ya ba shi sanin tarihin al’ummatai, Allah ya ba shi iya buga Misali, iya jagorancin al’umma, bujiman Malamai a fannonin Ilimai sun dauki maganar Annabi (SAW) a fannin ita ce hujja, kamar bangaren fassarar mafarkai, bangaren magunguna, kuma shi ne likitan zamaninsa.
Shehu Ibrahim Inyass ya ce, Annabi (SAW) shi kadai ya rike kusan fannonin Ilimi tara, kowanne fanni aka ba wa mutum daya, sai rayuwarsa ta kare bai kammala fannin ba.
Annabi (SAW) bayan kasancewar daya daga cikin Ulul azmi, ya shiryar da halitta ya gyara Larabawa, ya sauya su daga dabi’un da aka san su da su na alfahari da iyaye, yau sun koma alfahari da Musulunci, wadanda ake gani ‘yan kauye a da yanzun sun zama ‘yan birni har sun Mulki ‘yan birni da duniya baki daya. Manzo (SAW) ya ci nasara anan, Turawa da kansu suka fadi hakan.
Manzon Allah (SAW) ya shirya wa al’umma abin da ya gyara duniyarsu da lahirarsu. Bayan Annabta, Annabi (SAW) shugaban kasa ne, kwamndan yaki ne (shi ke shirya filin yaki), shi ne shehin zawiya an ce a rayuwarsa baki daya, sau biyu ko uku ne kadai bai yi limanci ba – Lokacin cutar ajali da wata rana a hanyar zuwa yakin Tabuka da wata rana yaje rabon Gado, Sayyadina Abubakar ya yi Sallah da Mutane.
Wata rana da dare, wani abu ya yi kara a wajen garin Madina, ana tsammnin yaki ne ya zo, kafin kowa ya isa wurin, Annabi (SAW) ya riga kowa isa wurin. Annabi (SAW) shi ya haskaka kwakwalwar sahabbai su kuma suka haskaka ta mutane har duniya ta zama haka. Shi ya hada mu a Tuta daya, kundin tsarin Mulki daya, Addini daya, wayewa daya, harshe daya.
Yana daga cikin kwarewar iya shugabancin Annabi (SAW), yana zuwa Madina bayan Hijira Masallaci ya fara ginawa, sabida shi ne wurin taro da zai hada kan mabiya tsakanin Muhajiruna da Ansaru. Shi ya fara kafa kundin tsarin mulkin kasa ta yadda kabilu daban-daban mabanbanta addini na kasa za su zauna da juna lafiya.
A cikin garin Madina akwai maguzawan Larabawa da Yahudawa da Nasara da Musulman Larabawa ‘yan asalin garin Madina (Aus da Khazraj) Ansaru da kuma wadanda suka yo Hijira tare da Annabi (SAW).
Manzon Allah (SAW) ya nuna mana yadda musulmi za su zauna a garin da ba addininsu ake yi ba kuma ana kin su (zaman Makkah) ya kuma nuna mana yadda ake zama a garin da ba a kin Musulunci amma kuma ba addinin Musulunci ake yi ba (Zaman Habasha, garin Najjashi) ya kuma nuna mana yadda ake zama a garin da ana son ka kuma ana Addinin Musulunci amma ba Musulmai ba ne kadai a garin (zaman Madina) Akwai Larabawa wadanda ba musulmai ba, akwai Yahudawa, akwai ragowar Nasara Najrana sannan kuma akwai shugaba a garin Madina (Abdullahi bin Ubayyi bin Salul). Har wata rana bayan sauran addinatai sun karya kundin tsarin mulkin kasa, an kore su yanzun Madina ta zama ta Annabi (SAW) da Sahabbansa su kadai, yanzun kuma Annabi (SAW) sai ya koya mana yadda za mu zauna a garin da muke da cikakken ‘yanci mu kadai.
Haka kuma, Annabi (SAW) ya koya mana yadda ake yakin kare kai da yakin raba fada ba yakin zalunci ba, Annabi (SAW) ya ce “Alkatilu wal maktulu finnari” da wanda ya kashe da wanda aka kashe duk ‘yan wuta ne (a yakin zalunci) amma duk wanda aka kashe shi kan kare kasarsa ko dukiyarsa dan Aljannah ne.
Kowanne mai fanni na Ilimi, za ka samu ya rike maganar Annabi (SAW) hujja a fanninsa, ita ce makurar fannin, za ka samu wani ilimi ya shige masa ya rasa yadda zai yi da mas’alar wurin, sai ka samu ya ji an ce Annabi (SAW) ya yi magana kan mas’alarsa kuma an samu amsar abin da ya buya.
Annabi (SAW), shi ya ba mu tarihin Shari’o’in Annabawan da suka gabata, shari’arsa ta shafe wasu ta tabbatar da wasu.
Daga cikin fannonin ilimi da masu fannin suka dauki maganar Annabi (SAW) ita ce hujja, akwai: fannin Ilimin fassarar mafarki da likitancin magani da ilimin Hisabi (Lissafi) da Ilimin sanin dangi da wasu da dama wadanda in sha Allah za muyi maganarsu in mun zo Babin da ke magana kan Mu’ujozozinsa (SAW).
Duk wadannan Ilimai babu wani Malami da ya koya wa Annabi su ko kuma suka yi bita tare, kai bari ma, Annabi (SAW) ba’uwa ne (bai iya rubuta ko karatu ba) har Allah ya ba shi Annabta ya bayyana lamarinsa sannan ya sanar da shi kuma ya karantar da shi. Duk wanda ya binciki tarihin Annabi (SAW) zai tabbatar da hakan.
Allah Ubangiji ya tabbatar da hakan da fadinsa “wa allamaka malam takun ta’alam, wa kana fadlullahi alaika azima” Allah Ubangiji ya sanar da kai abin da ka kasance ba ka sanshi ba, lallai falalar Ubangiji a gare ka tana da girma. Annabi (SAW), ba shi da rowa, abin da Allah ya sanar da shi mu ma sai ya sanar damu, “wayu allimukum malam takunu ta’alamun” yana sanar da ku abin da kuka kasance ba ku sani ba.
Hankali ba ya iya kididdige baiwar Allah a kan Annabinsa, Baki ya gaza wurin yin bayanin baiwar Allah a kan Annabinsa ta yadda za a iya ganewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp