Kamar dai yadda gwamnatin kasar Sin ta jima tana alkawarta burinta na bunkasa hadin gwiwa da kasashe kawayenta na nahiyar Afirka, ta hanyar bunkasa kawance, da tallafa musu ta dukkanin hanyoyin da suka dace, ta yadda hakan zai ba da damar kaiwa ga kafa alummar Sin da Afirka mai makomar bai daya, kamfanonin kasar Sin a nasu bangaren na yin duk mai yiwuwa, wajen ganin an cimma wadannan manufofi, inda a kasashen Afirka daban daban, ake ganin yadda kamfanonin na Sin dake ayyuka a can, suke zurfafa ayyukan inganta musaya, da ba da tallafi ga alummun wurin.
Ga misali a baya bayan nan, wani rahoton bincike da aka fitar a kasar Uganda, ya nuna yadda kamfanonin Sin ke dora muhimmancin gaske kan yaukaka kawance tsakanin su da alummun kasar, ta hanyar gudanar da ayyukan raya alumma, da kyautata zamantakewa.
Rahoton mai taken “Rahoton shekarar 2022 game da sauke nauyin tallafawa alumma da kamfanonin kasar Sin ke gudanarwa”, ya nuna yadda kamfanonin na Sin ke taimakawa alummun wuraren da suke gudanar da ayyukansu da kayayyakin kiwon lafiya, da na yaki da cututtuka, da na tallafin karatu, da horon samun kwarewar sanaoi da sanin makamar aiki, da ayyukan gyaran makarantu da dai sauran su.
Ko shakka babu, irin wadannan manufofi da matakai da kamfanonin kasar Sin dake kasashen Afirka ke aiwatarwa, suna taka rawar gani wajen ingiza ci gaban kasashen nahiyar, kamar yadda ake gani yanzu haka a Uganda, inda tuni irin wadannan ayyuka suka tallafa a fannonin raya harkokin sufuri, da makamashi, da gina ababen more rayuwar alumma.
A hannu guda, mahukuntan kasar Sin na kara jaddada aniyarsu ta cika alkawuran da tka dauka, na gudanar da manyan manufofin nan gudan takwas, wadanda Sin ta gabatar yayin taron dandalin ministocin Sin da na kasashen Afirka karo takwas, karkashin dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC, wanda ya gudana a shekarar bara a kasar Senegal, inda karkashin manufofin ake sa ran nahiyar Afirka za ta ci karin gajiya mai yawa daga kasar Sin, a fannonin samar da ababen more rayuwar jamaa daga dukkanin fannoni.