Abokai, yau “duniya a zanen MINA” na zura ido kan hanyar Duku dake yankin Xinjiang na kasar Sin, wadda aka kaddamar a kwanan baya, shimfidar wurin da wannan hanya ta ratsa na da nishandantarwa da kayatarwa sosai, har an iya ganin shimfidar wuri na lokacin bazara da zafi da kaka da kuma sanyi a yini daya idan ana tafiya kan hanyar, don haka, ta jawo dimbin baki masu yawon shakatawa daga gida da kuma waje, lamarin da ya sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin yankin.
Wannan hanya mai matukar mallakar shimfidar wuri mai kyau ta kuma ratsa yankin kudu da arewacin Xinjiang, don haka ta kuma kasance wani dandali mai inganci ga duniya wajen fahimitar yankin.
Sinawa kan cewa, idan ana son samun arziki, dole ne a gyara hanya. To idan ana keta hakkin dan Adam a Xinjiang tare da neman boye batun, me ya sa aka gina wannan hanya? (Mai zane: Amina Xu)