Assalamu alaikum! Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan fili namu na Ado Da Kwalliya.
A yau na shafin namu zai kawo muku hanyoyi goma wanda za a bi don gyaran jiki ba tare da an kashe kudi a shagon kayan kwalliya ba.
Ya kamata mata su koyi dabaru da dama domin taimaka wa maigida. Idan maigida ya saba ba da kudin sayen kayan kwalliya, ranar da babu kuma sai a hakura a gwada daya daga cikin ababen da muke kawo muku na gyaran jiki.
Na farko: Idan kin so ki gyara gashi za ki iya hada Ayaba da Kwai, sai ki kwaba su sosai sannan ki shafa a gashi ki barshi kamar tsawon ashirin minti 20 zuwa talatin 30, sannan ki wanke.
Na biyu, domin gyara fuska, za ki iya tsoma hannu a cikin man zaitun kamar na tsawon minti biyar 5 sannan sai ki cire ki shafa a fuskarki, ki yi kullum Fuskarki za ta yi matukar kyau sosai.
Na uku: za ki iya amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai santsi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon minti 15 zuwa 20, sannan a wanke da ruwan dumi. Ki gwada wannan hadin sau daya ma a sati za ki ga canji.
Na hudu: Ana amfani da ruwan Amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke makale a gefen gashin kai.
Na Biyar: Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rika shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka bakin da ya bayyana a wasu gabbai ko sassan fata.
Na shida: Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rika dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.
Na bakwai: Man kwakwa na matukar gyara zubewar gashi. Za a iya shafa man kwakwa a fatar kai, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.
Na takwas: Za ki iya yi wa maigida amfani da man kwakwa wajen gyaran gemu, yana matukar gyara gemu sosai.
Na tara: Za ki samu lemon tsami sannan ki zuba zuma a kai. Sannan ki rika shafawa a kan kurajen fuska. Yin hakan na kashe su sosai.
Na goma: Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata.