… ci gaba daga makon da ya gabata.
2. Samar Da Tsarin Da Za A Rika Saka Wa Malamai
Samar da tsare- tsaren bunkasa Malamai wata hanya ce da za a kara masu kwarin gwiwa saboda a matsayinsu na Malamai ba za su rasa wasu matakan da suke bukatar cimmawa a sana’arsu ta Malamai kamar bunkasa dalibai kara masu ci gaba da dai sauransu.
Idan da akwai hanyoyi na kara kwarin gwiwa domin cimma wasu manufofi kamar bada kyauta ga Malamai,wannan kuma al’amari ne wanda zai kasance da za a ci gaba da yn shi ne lokaci zuwa lokaci.
3. Ba Malamai Dama Na Bunkasa Fasaharsu
Taimakawa Malami ya kasance suna iya yin wani abinda zai kawo ci gaban aikinsu wannan ma wata hanya ce da ke sa kowane lokaci su zama shirin ko- ta-kwana,wajen bayar da gudunmawa mai dadewa ana cin moriyarta. Koyarwar da kowane lokaci akwai dabarun koyarwa ta amafani da kwarewa da kawo dauki, hakan na taimakawa dalibai su gane abin da ake koyawa masu sosai.Idan ya zama Malamai suna amfani da hanyar da za ta amfanar ta hanyar dabara da tunani na ilmantarwa duk lokacin da suka shigo aji koyarwa, irin hakan na daukar hankalin dalibai ko ‘yan makaranta al’amarin koyarwar tasu ya kasance sun a da sha’wa da maida hankali wajen samun ilmi.
Ba Malamai kwarin gwiwa su yi amfani da samar da hanyoyin ko dabarun koyarwa kamar yadda za’a gano amsa ko matsaya,matakin gamsarwa tare,irin hakan yana taimakawa dalibai, saboda ai za su gane darussan da ake koya masu kwarai da gaske ta hanyar koyarwa ta gwaji.Matukar har aka ba Malamai dama su rika koyarwa ta tunaninsu da fahimtar darasin ko daraussa wannan na samar da kafa da za su koyar da ingantacciyar hanya.
Alal misali Edmodo,kafar koyarwa ce da take taimakawa wajen ba Malamai kwarin gwiwa domin tana basu dama su rika musayar ra’ayi kan abu mafi kyau domin samun hanyoyin da suka fi kamata na koyarwa.Ta hanyoyi kamar su gudunmawar al’umma, musayar abubuwan amfani, masana ilmin Edmodo,musayar ra’ayi, tsarin yadda ake koyarwa,da yadda ake tunkarar hanyar koyarwa.Har ila yau kafar tana samar da yanayi maikyau inda Malamai za su koyi wani abu daga juna da yin gwaji da sabbin dabarun koyarwa da hakan zai taimaka matuka wajen kara inganta shigo da sabbin abubuwa a tsarin ilmi.
4. Kulawa Da Lafiya Da Jin Dadin Malamai
Kulawa da lafiyar Malaman makaranta al’amari ne mai muhimmanci wanda zai kasance wani abu ne da zai karfafa ko sa su Malaman su san aikin koyarwa.Hukumomi za su ba da kyakkyawar kulawa da lafiyarsu ta tsare- tsare da suka kunshi lafiyarsu da ta hankalinsu.
Wannan zai kunshi samar da yanayi motsa jiki da taro lokaci zuwa lokaci a kan yadda za ‘ay maganin gajiya, da yadda za a rika bada shawara.Ga kuma amfani da wata damar da ta kamata a bada ta yadda abubuwa su iya kasancewa daidai da daidai, ga kuma lokacin da za a samu dama ta hutawa, sai karuwar duk abubuwan da ka iya taimakawa samun lafiya ga ma’aikaci ba tare da wata wahala ba.
Wajen nuna da gaske ne ake na al’amarin da ya shafi kulawa da lafiya sai kamfanonin Edtech suka samar da wata dama ta taimakawa Malamai gabatar da aikinsu da gudunmawar da su kan bada, abin da daga karshe zai taimaka masu wajen inganta rayuwarsu.
Alal misali an san makarantar Khan wajen maida hankali kan lafiyar ma’aikatanta, sai kamfanin ya samar da wasu dabaru kamar bada shawara,taro na yadda mutum zai kula da lafiyarsa da karin hanyoyi na samar da daidaito na yadda Malamin makaranta ba zai cutu ba wajen kula da lafiyarsa.Da yake Shugabannin makarantar Khan sun fahimci matsalolin da suke tasowa ta bangaren ilmin fasaha, sai ya bullo da wani tsarin da zai tabbatar da ma’aikata sun samu dukkan abubuwan da suka dace da za su taimakama masu wajen samar da koshin lafiya da abubuwan da za su ci gaba da basu kwarin gwiwa.