Assalamu Alaikum ina muku barka da kasancewa dani a wannan filin namu mai suna GARKUWAR INTERNET kamar kullum yau zamu tattauna akan yadda zaka kare kanka daga Damfarar Yanar Gizo.
Shin ko kunsan a yau, amfani da intanet ya karu sosai, kuma hakan yana kawo matsaloli masu tarin yawa, musamman ga wadanda ba su da isasshen ilimi a kan kare kansu daga damfara. Ya kamata mu fahimci yadda masu cuta ke aiki don mu guje musu.
- Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji Kan KayayyakintaÂ
- Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji Kan KayayyakintaÂ
Yadda Damfarar Yanar Gizo Ke Aiki
Phishing (Damfarar E-mail da SMS): Ana aikawa da sakonni na bogi domin sace bayanan mutum kamar asusun banki.
Identity Theft (Satar Bayanan Mutum): Ana amfani da hotuna ko bayanan mutum ba tare da izini ba.
‘Fake Inbestment Schemes’: Masu cuta na amfani da shafukan zuba jari na bogi domin damfarar mutane.
Ransomware: Wasu barayin yanar gizo na saka kwayoyin cutar kwamfuta domin su hana mutum amfani da na’urarsa sai ya biya kudi.
Hanyoyin Kare Kanka
Yi amfani da kwayoyin kalmomin sirri masu karfi – A guji amfani da kalmomin sirri kamar sunanka ko shekarunka.
Yi amfani da Two-Factor Authentication (2FA) – Wannan yana 1ara kariya ga asusunka.
Guji danna hadin gwiwa (links) daga tushe da ba a san su ba – Yawancin wadannan hanyoyin suna da cutarwa.
Ka tabbata cewa shafin da kake ziyarta yana da alamar ‘https’ – Wannan yana nuna cewa shafin yana da kariya.
Kar ka raba bayanan sirrinka da kowa – Kar a taba bayar da PIN, OTP, ko wasu muhimman bayanai.
Labari Mai Karfafa Gwiwa
Akwai wata mata mai suna Zainab wacce ta samu sako daga wani wanda ya ce ta ci kyautar N500,000. Da yake tana da ilimi a kan Phishing, ta lura cewa sakon yana da alamun yaudara. Ta guji danna link da aka tura mata kuma ta sanar da abokanta domin su kare kansu. Wannan yana nuna cewa sanin dabarun kare kai a intanet yana da matukar muhimmanci.
Kammalawa
A duniyar intanet, dole ne kowa ya kasance cikin shiri domin guje wa damfarar yanar gizo. Mu kasance masu taka-tsantsan da duk wani bayani da muke rabawa a intanet. Kada mu yarda da komai da muke gani online sai mun tabbatar da gaskiyarsa.
Ku ci gaba da bibiyar wannan shafi don samun karin bayani kan yadda za a kare kai daga hatsarin intanet!
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp