Assalamu alaikum masu karatu barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai yi duba ne da yanayi, mun shigo yanayin sanyi ana samun matsalar bushewar fata.
- Sin Ta Yi Tir Da Matakin Amurka Na Sayarwa Taiwan Makamai
- Talauci Ya Sa Ake Samun Karuwar Matasa Masu Fasahar Waka A Nijeriya -Tiwa Sabage
Kaushin fata abu ne wanda ke addabar fatar mutum musamman a lokacin sanyi. Wasu za ku ga suna fama da bushewar fata musammam ma ta kafa, kafa tana kaushi.
Akwai ababen da ke sanya kaushin fata kamar yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi. Akwai nau’o’in mai da dama masu magance matsalar kaushin fata amma yawancinsu suna da tsada.
Domin bin hanya mafi sauki wajen magance wannan matsala ta fata ga sunan za mu lissafo kamar haka;
A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a bar ta tsawon minti biyar zuwa 10 kafin a shiga wanka a kullum. Sannan a rika diga man zaitun a cikin man shafawa. Yin hakan na sanya fata laushi kuma yana rage kaushin fata.
Za a iya kwaba fiya a shafa a jiki a bari na tsawon minti 15 sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko kuma a hada lemon fiya a rika sha domin magance kaushin fata.
A rika amfani da man kwakwa a fatar jiki, a dora man kwakwa a wuta ya dan yi dumi sannan a mulke fatar jiki na tsawon minti 30 kafin a shiga wanka, a rika yin haka a kullum. Sai kuma shan madara kofi daya kafin a kwanta barci kullum yana taimaka wa fata sosai.
A rika shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka da dare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gaba daya da man kadanya domin samun fata mai laushi kuma mai sheki.
A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya sannan a shafa a fuska ko fata na tsawon minti 20 sannan a wanke da ruwan dumi. Shi ma Lemon tsami da sukari na taimakawa wajen fitar da fatar da ke da gautsi a jiki sannan suna sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matse ruwan lemon tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti uku sannan a wanke.
A yi amfani da daya daga cikin ababen da na lissafo. Kada a shafa a lokaci guda don amfani da abubuwa da yawa na haifar da kuraje.