• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Warware Matsalolin Ma’aurata(1)

by Bilkisu Tijjani
6 months ago
Matsaloli

Ku himmantu da kaunar juna gaya, domin kauna ta kan yafe laifuka masu dimbin yawa.

Bayan aurenku, matsaloli daban-daban za su kunno kai.

 

Wadannan matsalolin suna iya tasowa a sakamakon bambancin ra’ayi da bambancin tunani da kuma yadda kuke tafiyar da rayuwa. Kari akan haka, matsaloli suna iya zuwa daga wurare daban-daban har da abubuwa na ba za ta.

Sannan kada ku kasance masu bayyanar da sirrin ko nace matsalolinku ga wani mutum na uku, domin hakan idan ba’a yi sa’a ba ya kan kara yawan matsala. Domin shi wannan mutum na uku da kuka sako shi cikin matsalarku idan ba’a yi sa’a ba ya yi muku shari’a ba ta gaskiya ba, za ku ga matsalolin za su karu.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Hadin Tsumin Baure

  • Ganduje Ya Nada Tsohon Kwamishinansa Garba, Shugaban Ma’aikatan Jam’iyyar APC 
  • Kamshin Jiki Da Cikar Hankalin Manzon Allah (SAW)

Maimakon mu guje wa matsalolin da muke fuskanta, ya kamata mu nemi shawarar magance su. Idan kuka bi ka’idodin hakan zai taimaka muku ku magance matsalolinku.

Ku tattauna matsala:

Akwai lokacin magana, Ku tabbata cewa kun tattauna matsalar sosai. Ka gaya wa matarka ainihin abin da ke zuciyarka da kuma ra’ayinka a kan batun. A kowane lokaci, ku gaya wa junanku gaskiya, ko da abin vacin rai ya faru kada ku yi fada. Idan ka yi maganar da za ta sanyaya zuciyar matarka ba za ku yi gardama ba.

Ko da ba ku jitu a kan wannan batu ba ku ci gaba da yi wa juna alheri da kyakkyawan zato, kada ku manta cewa ya kamata ku rika nuna wa juna kauna da ban girma, ku yi kokari ku sasanta matsalar da ke tsakaninku nan da nan, kuma kada ku ki yin magana da juna.

Shawara:

Ku keve lokaci don tattauna matsalar da ke tsakaninku, idan matarka tana magana, ka yi kokari ka kyale ta ta gama magana, idan ta gama, sai ka yi magana, ku saurara kuma ku fahimta

Ku kaunaci juna wajen ba da girma, kowa ya riga ba dan’uwansa.

Yana da muhimmanci ka kasa kunne da kyau sa’ad da matarka take magana, ka yi kokari ka fahimci ra’ayinta kuma ka yi hakan da juyayi da kuma tawali’u. Kada ka yi kamar kana saurara kawai, idan da hali ka bar abin da kake yi gabaki daya don ka saurari matarka sosai ko kuma ka tambaye ta ko za ku iya tattauna batun a wani lokaci. Idan kuka dauki juna a matsayin abokai maimakon abokan gaba, ba za ku yi garajen yin fushi ba.

Ko da abin da matarka take fada yana ci maka rai, ka ci gaba da saurarawa don ka fahimce ta ka mai da hankali ga abin da take nufi maimakon kalmomin da take furtawa. Ka lura da muryarta da kuma fuskarta yayin da take magana.

A cikin dukan aiki akwai riba, amma tadin baki ba ya nufa ko ina sai wajen tsiya, yanke shawara mai kyau kawai ba shi ne aikin ba. Kuna bukatar ku yi abin da kuka shawarta za ku yi, yin hakan ba zai kasance da sauki ba, amma za ku samu sakamako mai kyau. Idan kuka ba juna hadin kai, za ku girbi ‘amfanin wahalarku.

Kowannenku ya Kudura yin abin da zai iya yi don ku warware matsalar da ke tsakaninku a lokaci-lokaci, ku zauna ku bincika don ku ga ko kuna samun ci gaba a wannan batun.

Idan kai da matarka kuka yi kokari sosai, aurenku zai yi dadi maimakon daci. Kada ku ta da maganar da ta riga ta mutu, ku mai da hankali ga na gaba, idan kuka ba wa juna hadin kai kuma kuka bi ka’ida za ku iya warware duk wata matsala da ta kunno kai.Ka tambayi kanka.

Wace matsala ce nake bukatar tattaunawa da matata cikin gaggawa?

Me zai taimaka mini in fahimci ra’ayin matata a kan wannan batun?

To daga nan kun san abin da ya kamata ku yi, sai ku dau himma.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

September 27, 2025
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Next Post
Gwamnatin Yobe Ta Ƙaryata Rahoton Bayyanar Boko Haram A Babban Birnin Jihar

Gwamnatin Yobe Ta Ƙaryata Rahoton Bayyanar Boko Haram A Babban Birnin Jihar

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025
Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025
Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

October 13, 2025
NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

October 13, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

October 13, 2025
Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

October 13, 2025
Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA

Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA

October 13, 2025
Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba

Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba

October 13, 2025
Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano

Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.