Fadar shugaban kasa ta kara nanata cewa, Nijeriya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fi kyau a yanzu akan yadda ya sa meta a shekarar 2015.
A martanin da fadar Shugaban kasa ta mayar jiya ga wani editan jaridar Daily Trust, fadar shugaban kasar ta bayyana editan a matsayin wanda ya jahilci tarihin Kasa.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mai rubutun ya yi dai-dai da yadda ya ce, “Kamar yadda kowace kasa a duniya ke cikin mawuyacin hali, Nijeriya ma ba a barta a baya ba”
A cewarsa, “duk wani hasashe na cewa gwamnatin Buhari ba ta bar ‘yan Nijeriya a wuri mai kyau ba kamar yadda ta same su lokacin mulkin gwamnatocin baya – musamman kan bangaren tattalin arziki, tsaro da cin hanci da rashawa – wannan hasashe ne Kawai tsantsa.
Shehu ya mai da martani ne kan Ikirarin marubucin cewa a gwamnatin shugaba Buhari babu abinda ya canza daga gwamnatocin baya, hasali ma lamuran kara dagulewa su kayi.