Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Larabar nan cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma, kasar Sin ta kasance mai ba da shawarwari da aiwatar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.
Ranar 12 ga watan Satumba ita ce ranar hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta MDD. Mao Ning ta jaddada cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, ya kunshi ruhin hadin kai da hadin gwiwa da taimakon juna tsakanin kasashe masu tasowa. Ciyar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa gaba, zai taimaka wajen kiyaye muradun kasashe masu tasowa, da inganta ci gaban tattalin arziki, da zamantakewa da muhalli mai dorewa, da kuma samar da daidaito a duniya.
Mao Ning ta ce, kasar Sin tana sa kaimi ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa a fannonin rage talauci, da samar da abinci, da fasahar aikin gona, da kiwon lafiyar jama’a, da raya masana’antu, da sauyin yanayi, da samun moriyar ci gaban duniya da ma bunkasuwarta. (Ibrahim)