A Wani lamari mai kama da tatsuniya ko wasan kwaikwayo! Ta kaka za a ce masana’antar shirya Fina-finai ta Amurka (Hollywood) ta fara durkushewa, ta kama hanyar zama tarihi!
Dangane da kiyasin shafin intanet na the-numbers.com, ya nuna Amurka na samar da fina-finai kusan 26,000 kowace shekara; kasar da ke binta a baya, tana fitar da kusan 5,000. Bugu da kari, hada-hadar kudi na fina-finan da aka yi a Amurka ya kai dala biliyan 650 a cikin shekara daya. Kasa ta biyu a wannan jerin, tana da kusan dala biliyan 60 a shekara.
- Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci
- Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya
A ranar Lahadin da ta gaba ne, Shugaban Amurka, Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na sada zumunta, shugaban ya yi ikirarin cewa, masana’antar fina-finan Amurka “kimarta na durkushewa cikin sauri” kuma fitattun wurare da yawa a duk fadin kasar “suna cikin mawuyacin hali” saboda fina-finan da ake shiryawa a kasashen waje suna da rangwamen farashi.
Saboda haka, ya ba da izini ga Ma’aikatar Kasuwanci da Wakilin Kasuwancin Amurka su kakaba harajin kashi 100 bisa 100 a kan duk wani fim da aka shigo da shi cikin Amurka da wanda ake shiryawa a ƙasashen waje.
Wannan mataki ya haifar da gagarumar muhawara a duniya. Yayin da manufar ke da nufin farfado da Hollywood da karfafa shirya fina-finai na cikin gida. Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar?
Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirerren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da dala biliyan 1 a kudin tikitin shiga a kasuwar cikin gida kadai. Bugu da kari, wannan adadi, ya haura sama da dala biliyan 2 a kudaden shiga a duk duniya. Wannan abin a yaba ne, amma a wani bangare, Wannan rahoton kadai, zai iya fusata gwamnatin Amurka, ganin cewa, kasar tuni ta yi wa kasar Sin bakin fenti da cewa, ita ce babbar abokiyar hamayyarta a bangaren kasuwanci a duniya.
In ba a manta ba, da ma tun bayan rantsar da gwamnatin Trump, ya sha alwashin kakaba haraji kan duk hajojin da ake shigowa da su Amurka. Hukuncin da gwamnatin ta yanke, lallai ba shakka ba ta canja ra’ayi ba kamar yadda ta yi da sauran sanarwar haraji, wanda hakan ya tabbatar da cewa, yakin cinikayyar duniya har da fina-finai.
Tun ba a yi nisa ba, Amurkawa sun fara dandana kudar yakin cinikayya, inda farashin kayayyaki suka fara tsauri ga ‘yan kasar.
Don haka, akwai yiwuwar Amurkawa za su nisanta daga duk wani fim da aka shirya a ketare da zarar sun ga farashin tikitin ya yi tsada. Shin hakan zai iya zama abin da gwamnatin ke so?
Irin wannan hukunci da Amurka ke dauka, hakan yana da mummunan tasiri akan ‘yan kasarta ko da kuwa lamarin zai shafi sauran ‘yan kasashen waje.
Wai mu tambayi kanmu mana, Amurka ta rasa Dattawa da Masana ne wanda za su ba ta shawara kan harkokin tattalin arziki ne, ko kuwa Gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da shawarwarin su ne?
Masana da dama na ganin cewa, wannan mataki na zabga harajin kashi 100 bisa 100 a fina-finai zai haifar da mummunan sakamako ga masana’antar Hollywood, sannan kuma zai gurgunta kyakkyawar alakarta da takwarorinta na duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp