Dan Saran Kano Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya yi kira ga Gwamnati tarayya ta yi hattara a kan matakai da ake dauka da wanda ke dada tura al’ummar kasarnan cikin mawuyacin halin rayuwa.
Ya ce abubuwa sai dada tabarbarewa suke komai sai tsada yanzu ana maganar kara yawan haraji na kayayyaki wanda ba wani abu da zai haifar karawa al’umma r kuncin rayuwa.
- Sabuwar Ƙungiya Ƴan Ta’adda Ta Ɓulla A Sokoto – Shalƙwatar Tsaro
- Arsenal Ta Yi Barin Maki A San Siro
Ya ce wannan mataki na kara haraji duk da yan kasa da yan majalisu dama majalisar zartarwa ta kasa karkashin mataimakin shugaban kasa sun nuna rashin amincewa akai amma shugaban kasa Tinubu ya nuna yana kan bakansa wannan ya nuna ba maslahar yan kasa ake bukata ba.
Ya ce wannan ya nuna ba tsarin Damakwaradiyya ake bi ba a kasarnan domin idan tsarin ake bi ba da tsarin ake na gaskiya da aka ce kar a sa harajin nan shugaban kasa sai ya bi ra’ayin mutane masu rinjaye.
Alhaji Gambo Muhammad a ce yanzu tsarin Damakwaradiyya da ake kwaikwayo na Amurka idan a can ne an isa ayi haka? Shugaban kasa ya kamata ya sani zabar sa akayi don haka ya zama mai sassauci ga al’ummar kasa nan da shekaru Biyu zabe za a sake shiga ai sai a gyara yadda za a sassauta halin kunci da ake s ciki.
Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya ce kowa yasan halinda kara harajin nan na “VAT” zai jawo hauhawar farashi zai zama babu adadi ga kasa ba kudi a hannun al’ummar ta an tattare kudi basa a tsaya ayi abinda zai kawo sauki a kasarnan.
Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya yi kira ga yan majalisu da Sanatoci da Gwamnoni su takawa shugaban kasa burki ya sassauta ayi duba akan halinda al’umma suke ciki.Idan kowa zai san abinda yake ya tsaya ya zabi shugabanni masu kishin kasa da al’umma dole tallafawa su tashi su zabi mutane da suke da tausayi da kyautatawa talakawa.