Wasu ‘yan ta’addan Lakurawa, sun kai wani mummunan hari a garin Kalenjini, mahaifar Isa Kalenjini, shugaban karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, an kai harin ne jim kadan bayan shugaban karamar hukumar ya bar gidansa, wanda hakan ya sa mutane da yawa ke ganin cewa, shi aka kai wa harin.
- Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugaban Tsaro Da Ribadu Kan Kashe-kashen Rayuka
- Ƙasurgumin Ɗan Fashin Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Mutu Bayan Arangama Da ‘Yansanda A Kano
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Sokoto, Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, jami’an tsaro na hadin gwiwa sun bi sahun maharan.
Ya kara da cewa, an samu nasarar kwato wasu daga cikin dabbobin da aka sace a yayin farmakin bayan da maharan suka tsere zuwa dajin Tangaza.
Kokarin jin ta bakin Isa Kalenjini domin jin ta bakinsa ya ci tura, domin har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai amsa kiran wayarsa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp