Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago ya ba da tabbacin kare rantsuwarsa kan yaki da matsalar tsaro a Jihar Neja. Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin da yake jajanta wa al’ummar masarautar Kagara kan wani harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Garin Gabas da ke karamar hukumar Rafi.
Gwamnan Bago ya bayyana hakan ne a wata takardar manema labarai da mai taima wa gwamnan a bangaren labarai, Malam Boligi Ibrahim ya fitar a gidan gwamnatin jihar, inda ya bayyana cewa gwamnan ya yi mamakin kai harin da ‘yan bindigar su ka yi.
Ya jajanta wa ‘yan’uwa da iyalan wadanda abin ya shafa, sannan ya ce jama’a su fahimci gwamnatinsa, baya kawar da idanu a kan duk wani abu da ya shafi tsaro wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.
Ya ce jama’a su zama masu sanya idanu a kan abin da ya shafi tsaro, kuma su tabbatar sun gaggauta sanar da wadanda ke da alhakin tsaro domin daukar matakin gaggawa da zarar sun ga lamarin da ba su amince da shi ba.
Gwamna Bago ya ce zai ci gaba da karfafa gwiwar jami’an tsaro wadanda ke tsaye wajen ganin sun kawar da ‘yan bindiga, saboda samar da ingantaccen tsaro da walwala da jin dadin jama’ar jihar.
Ya yi addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga jami’an tsaro biyu da suka samu raunuka da kuma tabbatar da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.