Daya daga cikin mawakan da ke tasowa a yanzu cikin masana’antar Kannywood, OKASHA IBRAHIM MU’AZU Wanda aka fi sani da OKA DAN ALHAJI. Ya bayyana wa masu karatu irin kalubalen da ya fuskanta bayan ya fara waka tare da irin burikan da ya ke da su game da waka, har ma da sauran batutuwan da suka shafi sana’arsa ta waka. Ga dai tattaunawar tare da LUBABATU AUTA INGAWA Kamar haka:
Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanka, tare da takaitaccen tarihinka
Da farko dai sunana Okasha Ibrahim Mu’azu, wanda aka fi sani da Oka Dan Alhaji mawaki a msana’antar Kannywood. An haife ni a Jihar Katsina a karamar hukumar Bakori, a wani kauye mai suna unguwar Shantali. Na yi karatun firamare a cikin gari unguwar Shantali, nayi Sakandare a cikin garin Bakori.
Za ka kai kamar shekara nawa da fara waka?
Na fara waka a shekara ta dubu biyu da sha takwas wato 2018.
Ya ka dauki waka a wajenka?
A gaskiya ni na dauki waka a matsayin sana’a.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ya kasance?
Gaskiya kuwa na sha kalubale daban-daban, musamman alakar mu da mutane ta yadda wasu suke kallonmu a marasa tarbiyya, musamman na jikiinmu
Idan na fahimce ka daga Iyaye, ‘yan uwa da abokai ka samu wani sauyi na zamantakewa da suka yi sanadiyar fara waka?
A gaskiya ni ban samu wata damuwa daga iyayena ba, kasancewata mawaki, amma a cikin ‘family’ dinmu na fuskanci kananun maganganmu wanda ya sa har yanzu ana ganin aikin banza nake yi, wasu ma daga cikinsu suna ganin shurme na kawai nake yi.
A ganinka wanne dalili ne ya sa har yanzu suke kallon shirme ka ke yi, Baka samu wani canjin rayuwa bane tun da ka fara wakar ko kuwa akwai abin da ka ke yi na kasuwanci ko karatu, amma ka daina yinsu silar wakar da suke yi maka kananun maganganu?
Su kansu yanzu haka lokaci ya fara nuna masu cewar wakar da nake yi ba shirme bace ba, tunda har sun fara jin nasu ne musamman idan suka yi nisa da gida su ji yankin suna sauraren wakokina. Maganar karatu kuma ko kasuwanci duk ba daya daga ciki da za su yi tunanin waka za ta hana ni gudanar da su, kuma koda su basu sani ba wasu sunan cewa kasuwanci ai shi ne jigon karamin mawaki.
Da wacce waka ka fara ya karbuwar wakar ta kasance ga su masu saurara?
Eh! wakata ta farko ita ce; Wakar Zainab kuma Alhamdulillah lokacin da na yi wakar wasu ma cewa suke wai ba ni na yi ta ba, saboda mamakin da sukai ace wai yau Oka ne yake waka abin ya basu mamaki sosai fa, daga nan kuma sai mutanen garinmu suka yi tayin tururuwa zuwa wajena domin na tura masu wakata.
Sunan wakarka ta farko Zainab. Akwai wata Zainab da ka ke da alaka da ita ne wadda dalilinta ya sa kayi wakar ko kuwa ya abin ya ke?
Eh! gaskiya a wannan lokacin ina tare da Zainab sakamakon haka ne ma ya sa nayi wa Zainab waka.
Zainab din ‘yar uwa ce ko Budurwa, Ya ya alakarka take da ita da kuma bayan ka fara wakar?
Abu ne ya zama guda biyu a lokacin wanda har kawo iyanzu wasu na yin maganganu, sakamakon rabuwata da wata ‘yar uwa mai suna Zainab, wadda a lokacin iyayenmu suka so na aureta har baiko da sa rana aka yi amin da ita, to bayan munrabu da ita kuma sai na fara soyayya da wannan zainab din da nayi wa waka.
Kana da ubangida a cikin masana’antarku?
Gaskiya ba ni da ubangida a harkar waka
Da wanne mawaki ko mawaki ka fi so kayi waka?
Eh! gaskiya ina son yin waka da Fati Niger sannan kuma ina son yin waka da Hamisu Breaker ko dan masoyanmu, sakamakon dubban mutane suna ganin kamannin da muke yi wasu ma suna tunanin ni da shi ‘yan uwa ne.
Mene ne yake birgeka a cikin wakokin Hamisu Breaker da na Fati Niger wanda har ya ja hankalinka ka ke son yin waka da su?
Gaskiya Fati Niger mawakiya ce wadda na dade ina jin wakokinta muryarta ta fita daban a cikin mata mawaka, shiyasa nake son na yi waka da ita, sakamakon duk wanda ya ji ya san ita ce, shi kuma Hamisu ta yadda salonmu ya zo daya da har ya sa idan nayi hoto ko bideo masoyansa suke bibiyata da son ganina a koda yaushe. Sannan kuma a cikin gidan mu ko iyayena idan za su yi magana akan Hamisu sai su musaltashi da ni, hakan ya sa na ji ina son yin waka da shi, sannan kuma masoyanmu suma suna bukatar hakan.
Bayan waka kana yin fim ne, ko kana sha’awar shiga fim?
Gaskiya bana yin fim kuma bana sha’awar yin fim.
Mene ne burinka na gaba game da waka?
Ina son a duk inda na shiga a ce Oka Dan Alhaji, kuma ina son na daukaka a harkar waka idan Allah ya sa ina daga cikin masu daukaka.
Wacce irin mace ka ke son aura?
Ina son mace wadda ta san darajar kanta kuma ta san darajar dan Adam.
Wanne irin abinci da abun sha ka fi so?
Abinci ina son Dan Wake sosai, abun sha kuma ina son Multina sosai.
Ya alakarka da sauran abokan aikinka?
Muna zaune lafiya da ganin mutuncin juna, muna rayuwa cikin aminci da kulawar junanmu.
Wacce shawara za ka bawa masu kokarin shiga masana’antar dan fara waka?
Eh! to ga dukkanin mai son ya shiga wannan masana’antar to gaskiya abu biyu ne zuwa uku na farko yaddar iyaye, na biyu hakuri na uku tsabtace harshenka zuwa zuciyarka.
Me za ka ce ga masu yi wa mawaka mummuna kallo?
Su ji tsoron Allah kuma kafin su yi zagi a gare mu su fara duba nasu laifin, sannan sai su yi wa kansu hukunci domin mawaki ko dan fim ba hakan yana nufin cewa sun kauce hanya bane, kowacce irin sana’a tanada wuta kuma tanada aljanna kuma ko kai malami ne ko sabanin hakan.
Ko akwai wani kira da za ka yi ga gwamnati game da ci gaban mawaka?
Gaskiya ne yanada kyau gwamnati ta san cewa a harkar waka ko fim muna bukatar tallafi da kuma nuna amincinta a cikin harkar, saboda muma muna son ci gaban da sauran kasashe suka samu daga wannan masana’anta, ina mai jan hankalin gwamnati da ta kara inganta harkar ko dan samun ci gaban kasata.
Me za ka ce ga makaranta shafin Rumbun Nishadi?
Ina yi masu fatan alkairi kuma da sakon gaisuwa a gare su, sannan ga dukkanin me bukatar wakokina ya biyoni ta audiomack mai suna [email protected] ko Oka Dan Alhaji TB, na gode sosai.
Me za ka ce da ita kanta Jaridar Leadership Hausa?
Wannan jarida ina matukar godiya a gare ku, kuma ina rokon Allah ya kara daukaka ta Allah ya taimaka, sannan wannan shirye-shiryen da ku ke yi Allah ya kara dankon zumunci.
Amin summa amin muna godiya da wannan addu’a, Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Ina gaida Aunty aisha wadda ta hada ni da ku, ina yi mata fatan alkairi. Sannan ina mika gaisuwa ga Bilkisu wadda bana ce komai a kanta ba, sannan ina gaida dukkanin masoyana dake fadin duniya baki daya.
Muna godiya da kasancewa tare da mu daga farko har izuwa karshen wannan Tattaunawa.
Ni ma na gode sosai da kasancewar da ku ka yi tare da ni domin tattaunawa.