Akalla mutane biyar ne a ranar Laraba suka mutu yayin da wasu 10 suka samu raunuka a wani hatsarin da ya faru a hanyar Legas zuwa Ibadan.
Lamarin ya afku ne a kwanar NASFAT da ke kan babbar hanyar da misalin karfe 10 na dare, inda ya rutsa da wata mota kirar Daf mai lamba KUT 561 ZZ da wata motar bas Toyota Hiace mai lamba GGE 84 YF da kuma wata tankar mai mara lamaba dauke da man dizal.
Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Ogun, Misis Florence Okpe ce ta tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin a Abeokuta, babban birnin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp