Wani hatsarin mota mai muni ya auku a jihar Bauchi a yau Lahadi, inda manyan motoci suka yi taho mu gama, wanda ya janyo mutuwar wani matashi mai shekara 23, Usman Magaji, da kuma raunuka ga wasu biyu.
Hatsarin ya faru ne a garin Magama Gumau, inda ɗaya daga cikin manyan motocin da ke ɗauke da yashi da mutane hudu ciki ta yi karo da wata motar da ta lalace. Hakan ya haifar da tashin wuta, inda dukkanin motocin biyun suka kama da wuta kuma suka ƙone ƙurmus.
- Fedpoly Bauchi Ta Sanya Na’urorin Ɗaukan Hoto ‘CCTV’ Don Daƙile Satar Jarabawa Da Inganta Tsaro
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Satar Mota A Bauchi
Jami’an tsaro, ciki har da Ƴansanda daga ofishin Magama Gumau da sauran hukumomi, sun yi gaggawar kai ɗauki zuwa wajen lamarin domin kashe wutar da kuma ceto waɗanda suka ji rauni. An tura waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Toro domin samun kulawar likita, amma likita ya tabbatar da mutuwar Usman Magaji.
Kakakin rundunar Ƴansandan jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin da Kwamishinan Yiansandan jihar, CP Sani-Omolari Aliyu, ya yi jaje ga iyalan mamacin.
Ya kuma jaddada muhimmancin bin dokokin tuki, musamman sanya alamar motar da ta lalace akan hanya don janyo hankalin direbobi, tare da umartar sashin kula da hatsarin motoci (MTD) da su zurfafa bincike kan hatsarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp