Wata mota ƙirar Toyota Hiace mai ɗaukar fasinjoji ta ƙwace kuma ta kutsa cikin kasuwa a Damagum, Jihar Yobe, inda ta kashe mutum biyar tare da jikkata wasu 19.
Kwamandan Hukumar FRSC a jihar, Livinus Yilzoom, ya tabbatar da cewa hatsarin ya faru ne da yammacin Lahadi, lokacin da mutane ke cin kasuwa a gefen hanya.
- Ya Kamata Lambar Yabo Ta Zama Hanyar Ƙarfafa Mana Gwuiwa – Misis Nda-Isaiah
- Sin Za Ta Mai Da Martani Kan Barazanar Kara Kakkaba Mata Harajin Kwastam Daga Amurka Â
Ya ce waɗanda suka mutu ba fasinjojin motar ba ne, sai dai ‘yan kasuwa da masu sayayya da ke bakin hanya.
Bincike ya nuna cewa gudu fiye da ƙima ne ya sa motar ta ƙwace wa direban.
Wasu da suka ga lamarin sun koka da yadda ake gudanar da kasuwanci a gefen babbar hanya, suna mai cewa hakan yana haddasa yawan haÉ—ura.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp