A yau ne, hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da wata sanarwa game da yawan hatsin da aka samar a shekarar 2022 da muke ciki.
Dangane da samfurin bincike da aka gudanar a larduna 31 na yankuna da biranen fadin kasar da kuma cikakkiyar kididdiga na kamfanonin aikin noma, a shekarar 2022, jimillar hatsin da aka samu a noman rani, da shinkafa da hatsi a lokacin kaka a larduna 31 da ya kunshi yankuna da birane, zai kai kimanin kilogram triliyan 0.68, wanda ya karu da kilogram biliyan 3.7, wato ya karu da 0.5% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, wanda ya kai sabon matsayi. Wannan ita ce cikin shekaru takwas a jere, jimillar hatsin da kasar Sin ta samar ya kai fiye da tiriliyan 0.65. Daga cikin su, yawan hatsin da aka samar ya kai fiye da kilogram triliyan 0.63, wanda ya karu da kilogram miliyan dari 5 bisa na shekarar da ta gabata.
Tun farkon bana, kasar Sin ta dauki kwararan matakai masu amfani wajen tabbatar da samar da isassun kayayyaki, kamar takin zamani da maganin kasha kwari da irin shuke-shuke da dai makamatansu, wadanda suke shafar zaman rayuwar yau da kullum na jama’a da farashinsu, ta yadda ta tabbatar da ganin yawan amfanin gona ya karu.
Farashin kayan abinci a cikin gida ma bai haura ko sauka fiye da kima ba. Sakamakon haka, kasar Sin ta tabbatar da ganin an biya bukatun zaman rayuwar jama’a, da kuma karfafa hasashe da imanin da ake da su a kasuwa kamar yadda ya kamata.
Kasar Sin da yawan gonakin da take da shi ya kasa da kashi 10% bisa na jimillar gonakin duk duniya, amma ta samar da kusan kashi 25% na hatsin da ake nomawa a duniya kuma tana ciyar da kusan kashi 20% na al’ummar duniya.
Wannan girbi mai yawa ya samo asali ne sakamakon hadin kan al’ummun Sinawa baki daya wajen daukar nauyi na samar da isassun kayayyakin abinci da kansu, lamarin da ya nuna aniyar kafa wani tushe na tsaron abinci bisa dukkan alamu, kuma yana karfafa kwarin gwiwar al’ummun Sinawa wajen tsayawa tsayin daka kan matsayin samar da isassun kayayyakin abinci da kansu. (Safiyah Ma)