Ya zuwa yanzu, kwanaki 8 ke nan, amma, ba a kashe gobarar dajin da ta tashi a tsibirin Maui na jihar Hawaii ta kasar Amurka ba. Mutane sun fara mamaki cewa, me ya hana Amurka dake da tsarin aiwatar da aikin ceto mafi inganci da tsarin yin gargadi kan bala’u ta yanar gizo mafi girma a duniya wajen kashe wannan wuta?
Kamar yadda muka sani, jihar Hawaii tana da tsarin jiniya mafi girma a duniya, amma, mazauna wurin sun ce ba su samu sanarwar gargadi ba a lokacin da gobarar ta tashi.
Dangane da wannan batu, gwamnatin kasar Amurka ta kasa fitar da bayanan da za su gamsar da al’umma, sabo da bayan aukuwar bala’in, sojojin Amurka kimanin dubu 40 dake zaune a sansanin sojan kasar a jihar Hawaii su ma ba su yi aikin ceto cikin lokaci ba.
Kana, har zuwa yanzu, ba a kashe gobarar da ta tashi a gundumar Maui ba, sakamakon karancin kudi da masu aikin ceto, kamar yadda aka bayyana cikin rahoton rigakafin tashin gobara na gundumar Maui. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp