Ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin, ta sanar a jiya Asabar cewa bisa gayyatar da gwamnatin Birtaniya ta yi masa, memba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, zai ziyarci Birtaniya tun daga yau Lahadi har zuwa Juma’a 13 ga watan nan na Yuni.
Ana sa ran yayin ziyarar tasa a Birtaniya, He Lifeng zai halarci taron farko na tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. (Saminu Alhassan)