Hukumar kula da zirga-zirgar jirgen kasa ta kasar Sin ta bayyana cewa, yawan zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Sin da Turai, ya karu da kaso 18 cikin 100 cikin shekarar da ta gabata, wanda ya kai tafiye-tafiye 1,585 da ba a taba ganin irinsa ba.
A cewar hukumar, kimanin sassa 154,000, daidai da tsayin kafa 20 na kayayyaki ne, aka yi jigilar su ta cikin jiragen dakon kaya a watan Agusta, sama da kashi 19 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata.
A cikin watanni 8 na farkon bana, adadin tafiye-tafiyen jiragen kasa tsakanin kasar Sin da Turai, ya karu da kashi 5 cikin 100 bisa makamancin lokacin shekarar 2021, zuwa 10,575.
Haka kuma Jiragen kasan, sun yi jigilar kayayyaki da yawansu ya kai sassa miliyan 1.02, wanda ya karu da kashi 6 cikin 100 daga shekarar da ta gabata. (Ibrahim)