Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kano sun yi nasarar kuɓutar da wasu ‘yan mata 16 daga hannun wasu da ake zargin masu safarar mutane ne a tashar motar da ke Unguwa Uku a Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su ƙananan yara kan hanyarsu ta zuwa Legas, inda za a yi safarar su zuwa Jamhuriyar Benin da Ghana.
- Hisbah Ta Yi Kakkausan Gargaɗi Tare Da Kira Ga Iyaye Kan Kula Da Yara Bayan Samun Gawar Wasu 4
- Kwankwaso Ya Soki Ƴansandan Kano, Ya Buƙaci A Girmama Ƴancin Kano
Da yake jawabi mataimakin kwamandan Hisbah, Mujahid Aminuddeen Abubakar, ya ce, “Jami’an mu a tashar mota sun kama wasu mutane da suke yunkurin safarar waɗannan ‘yan mata masu ƙarancin shekaru. Wasu za su iya rasa rayukansu, yayin da wasu za a sayar da su, a tilasta musu yin karuwanci, ko kuma a bautar da su”
Abubakar ya bayyana cewa ‘yan matan da aka ceto ba su da masaniya kan illolin da za su fuskanta. Dukkansu sun fito daga ne arewacin Nijeriya, daga jihohin Kano da Katsina da Jigawa, da kuma jihar Borno.
Ya kuma buƙaci iyaye da su kara taka tsan-tsan tare da ba da fifiko ga tsaron ‘ya’yansu, yana mai gargadin kada su jefa su cikin irin wannan haɗari domin samun kuɗi.
“Dole ne iyaye su ɗauki nauyi kuma su kare ’ya’yansu. Yarda da fataucin su wani nau’in bauta ne na zamani wanda ke da mummunan sakamako,” in ji shi.
‘Yan matan da aka ceto yanzu haka suna hannun hukumar Hisbah, inda suke aiki da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da tsaron lafiyarsu da kuma gyara su.