Hukumar Hisba a Jihar Yobe ta samu nasarar damke akalla mutum 14 da ake zirgi da aikata fasikanci da kuma ta’ammuli da miyagun kwayoyi a lokacin azumin watan Ramadan.
Kwamishinan harkokin addini na Jihar Yobe, Alhaji Yusuf Umar, shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da Jaridar LEADERSHIP a Damaturu.
- Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL
- Ba Za A Iya Dakatar Da Dunkulewar Kasar Sin Ba
Umar ya bayyana cewa hukumar Hisbah tare da hadin gwiwar rundunar ‘yansanda sun samu nasarar kama wadanda ake zargin ne a wani samame da suka kaddamar a jihar.
 Ya ce wadanda ake zirgin sun kasance mata 9 maza 5, inda aka kama su suna aikata laifukan da suka saba da koyarwar addinin Musulunci a lokacin azumin watan Ramadan.
Umar ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda ake zargin za a mika su ga hukumomin tsaro domin gurfanar da su a gaban kuliya, yayin da sauran kuma za a mika su wurin malamai domin su yi musu wa’azi.
Ya dai shawarci al’ummar jihar, musamman ma matasa su yi watsi da aikata muyagun laifuka da za su iya kassara rayuwarsu nan gaba tare da habaka abubuwan da za su iya lalata zamantakewa.
Haka kuma kwamishinan ya yaba wa mazauna jihar bisa irin goyon baya da suke bai wa hukumar Hisbah wajen gudanar da ayyukansu, inda ya sha alwashin cewa hukumar Hisbah za ta ci gaba da yaki da badala a dukkan sassan jihar baki daya.