Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sakkwato, ta ce ta yi wa maniyyata aikin hajjin bana 3,918 rajista don tafiya aikin hajji kasar Saudiyya a shekarar 2024, daga cikin kujeru 5,001 da aka ware wa jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Aliyu Musa-Gusau, ya bayyana hakan bayan wata ganawa da jami’an mataimakan aikin hajjin na kananan hukumomi 23 a ranar Asabar a Sokoto.
- Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
- Sojoji Sun Mikawa Gwamnatin Sokoto Mutane 66 Da Aka Ceto A Jihar
Musa-Gusau, wanda ya samu wakilcin Daraktan gudanarwa na hukumar, Alhaji Ladan Ibrahim, ya ci gaba da cewa hukumar za ta rufe karbar kudaden yin rijistar aikin Hajjin 2024 a ranar 12 ga watan Fabrairu.
A cewarsa, rufe rajistar shekarar 2024 ya dogara ne da umarnin hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) na cewa a kammala dukkan biyan kudade da kuma sayen kujera zuwa ranar Litinin 12 ga watan Fabrairu.
Ya yi gargadin cewa duk mutumin da ya kasa kammala biyan kudinsa bayan ya ajiye kudi har Naira miliyan 4.5, ko kuma ya biya duka Naira miliyan 4,699, zai iya rasa aikin Hajjin bana.
Shugaban ya bayyana cewa maniyyata 1,806 sun biya Naira miliyan 4.5 zuwa sama, yayin da mahajjata 2,895 suka biya kasa da Naira miliyan 4.5.
Don haka, ya bukaci masu ajiya da su yi kokarin kammala biyansu, ko kuma masu son biyan duka kudin kafin ranar Litinin.