Gwamna jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ƙaddamar da wasu sabbin motocin sufuri mallakar gwamnatin jihar domin ƙara bunƙasa harkar sufuri a jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.
Da yake duba sabbin motoci gwamna Aminu Bello Masari ya yaba da ƙoƙarin hukumar sufuri ta KTSTA wajan samar da sababbin motocin kirar ‘Hummer’ duk ƙarshen wata.
Haka kuma gwamnan ya yi fatan hukumar zata cigaba da wannan namijin ƙoƙari wajan ganin an sauƙaƙa harkar sufuri a jihar Katsina.
Shima da yake nasa jawabin shugaban hukumar sufuri na jihar Katsina Haruna Musa Rugoji ya ce wannan nasara ta su ta samo asali daga irin gudummawar da gwamna Aminu Bello Masari ya ke ba su duk lokacin da bukatar haka ta ta so.
Ya ƙara da cewa wannan ƙaddamar da motoci suna yin sa duk bayan watanni uku ma’ana dai suna sayan mota guda duk wata sai bayan wata uku sai a ƙaddamar.
Alhaji Haruna Musa Rugoji ya cigaba da bayanin cewa bisa al’ada duk lokacin da suka sayi motoci suna kawowa gwamna Masari domin ya gani ya kuma sanya albarka kafin su ɗora su akan hanya domin cigaba da aikin al’umma
“Daga lokacin da na zo wannan hukuma a matsayin shugaba, mun samu nasarar sayen irin wannan motar kirar Hummer 31 sannan mun sayi motocin gudanarwa da kuma ta ofishin shugaban hukumar ” inji shi
Daga ƙarshe ya yi fatan ƙara inganta harkar sufuri a jihar Katsina ta hanyar cigaba da sayen motoci duk wata kamar yadda suka saba yi inda ya ce ta haka ne za a Iya gamsar da abokan hulɗa.