Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), ta rufe shaguna biyu da ke dauke da magunguna marasa rajista da ka iya ba wa kwakwalwa damuwa da darajarsu ta kai Naira miliyan 15 a farashin kasuwa.
Rahoton da gidan rediyon Nijeriya ya fitar, ya bayyana cewa a wani samame da aka gudanar a daya daga cikin wuraren da ke tashar mota ta Zuba a babban birnin tarayya Abuja, hukumar NAFDAC ta gano wani shago cike da magunguna marasa inganci da rajista.
Mataimakin darakta mai kula da bincike da tabbatar da doka na NAFDAC, Mr. Tamanuwa Andrew Baba, ya ce galibin magungunan ko dai kwanakin ingancinsu ya kare ko ba a yi musu rijista ba ko kuma suna da babbar illa.
Ya ce magungunan masu suna “Hajiya Aisha” ko “Hajia Salama” da aka gano ana fasa kwaurinsa daga kasar Ghana na dauke da wani sinadari mai suna “Pyridine” da ke haddasa cutar daji da sauran cututtuka.
A wani samame na biyu kuma a kasuwar Utako da ke Abuja inda aka kama magungunan ‘Aphrodisiac’, Mista Andrew Baba ya ce irin wadannan kwayoyi sun yi sanadin mutuwar mazaje da dama.
Ya bukaci maza da su nemi magunguna masu inganci daga ingantattun cibiyoyin lafiya don magance matsalolin da suka shafi jima’i.
Yaron shagon da aka cafke a Utako, Isah Sani ya ce su kan siyo magungunan ne daga Legas da Kano da sauran sassan kasar nan.