Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), a ranar Talata, ta fara rabon kayan abinci da cibiyar agajin jin kai ta Sarki Salman (KSrelief) ta bayar ga iyalai 2,056 a jihar Kano.
Shugabar hukumar NEMA, Hajiya Zubaida Umar, a lokacin da take kaddamar da rabon kayayyakin a Kano, ta ce, an yi hakan ne domin tallafa wa marasa karfi, da kuma dakile tsadar rayuwa.
- Zargin Hannu A Ta’addanci: Sheikh Gumi Bai Fi Ƙarfin Doka Ba, Tuni An Sallameshi Bayan Yi Masa Tambayoyi – Gwamnati
- Mutane 11 Sun Rasu, 30 Sun Jikkata A Rikicin Kabilanci A Filato – Gwamnati
NAN ta rahoto cewa, kungiyar KSrelief na bayar da agajin jin kai ga mabukata a wajen iyakokin masarautar.
Shugabar Hukumar ta NEMA, wacce Darakta ce a bangaren ayyuka na musamman ta wakilta, Hajiya Fatima Kassim, ta ce, tallafin abincin ya zo kan lokaci, domin ya zo daidai da watan Ramadan.
Ta ce “kowane gida zai samu kayan abinci, da suka hada da shinkafa (25kg), wake (25kg), masa vita flour (4kg), tumatur (2kg), man gyada (lita 2), maggi (0.8kg) da gishiri 1kg.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp