A sanyin safiyar Lahadi ne ambaliyar ruwa ta mamaye wasu kauyukan masarautar Argungu da ke jihar Kebbi, inda ta lalata gidaje fiye da 200 a masarautar.
Dangane da wannan iftila’in, Shugaban Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Kebbi (SEMA), Barista Bello Yakubu (Rilisco) ne ya jagoranci tawagar manyan jami’an gwamnati da suka hada da Mataimakin Gwamnan Jihar domin kai ziyara kauyukan da abin ya shafa tare da bayar da agajin gaggawa.
- Gwamnan Filato Ya Ƙaƙaba Dokar Hana Fita Ta Awa 24
- Tuntuni Muka Yi Gargaɗin Cewa, Zanga-zanga Za Ta Iya Zama Hargitsi – Minista Idris
Rilisco da tawagarsa sun ziyarci garuruwan Bayawa, Tiggi, Fakon Sarki, da unguwar Kara da ke cikin garin Argungu, inda suka tantance barnar da ambaliyar ruwan saman ta yi tare da raba kayayyakin agaji ga mutanen da abin ya shafa. Kayayyakin da aka bayar sun hada da kayan abinci irin su Shinkafa, Wake, Gero, Masara, da kuma abubuwan da ba na abinci ba kamar su man gyada, gidan sauro, sabulu, robobi, katifu, da barguna.
Haka Kuma, Barista Yakubu ya jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da tabbatar musu da kudirin gwamnatin jihar na bayar da tallafi a wannan mawuyacin lokaci. Ya kuma bukaci mazauna yankin da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu, inda ya yi alkawarin cewa, gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an dakile illar ambaliyar a yankunan nasu,
Mataimakin gwamnan wanda ya raka shugaban SEMA, ya kuma jajanta wa wadanda abin ya shafa, ya kuma yaba da kokarin hukumar bada agajin gaggawa na daukar matakan shawo kan bala’in. Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatin jihar za ta hada gwiwa da hukumomin tarayya domin bayar da karin tallafi da taimako.
An raba kayan tallafin ga kauyukan da abin ya shafa, inda kowane kauye ya samu kaso mai kyau na kayayyakin da aka bayar. Mazauna yankin da suka yi ta kokawa kan yadda ambaliyar ruwan ta afku, sun nuna godiya ga gwamnatin jihar da kuma hukumar SEMA bisa daukar matakin a kan lokaci.
Ziyarar da gudunmawar kayan agajin da Shugaban Hukumar SEMA da tawagarsa suka kai, ya sanya wa mutanen da abin ya shafa fatan alheri, inda a yanzu suka fara sake gina rayuwarsu bayan da aka yi mummunar barnar ta ambaliyar.