Shugaban hukumar ilimin bai daya ta Jihar Bauchi (SUBEB), Alhaji Adamu Mohammed, ya yi kira da al’umma/ iyayen yara da cewa su dauki lamarin sa ’ya’yansu wani babban abu ne da yakamata su bashi matukar muhimmanci.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a taron kwana daya da yake da muhimmanci saboda ya shafi lamarin amfani ne da tsarin mai suna Teaching at the Right Lebel (TaRL) (ko kuma koyarwa ta hanyar da ta dace, wanda aka yi a Bauchi.
- Babban Taron Lauyoyi Na Kasa: Sarkin Musulmi Ya Gargadi Alkalai Kan Tabbatar Da Adalci
- Cire Tallafin Wutar Lantarki Zai Kara Kuntata Rayuwar ‘Yan Nijeriya – Kungiyar Kwadago
Alhaji Mohammed ya nuan rashin jin dadinsa a wasu kura- kuran da ake yi na al’amarin koyarwa, inda yace wasu Malaman basu cancanci su koyar da masu koyo ba ta kowane mataki na koyon ilimi.
Ya yi kira da hukumar ta bada agajin gaggawa na lamuran kananan yara,ta UNICEF- TaRL ta kara fadada ayyukan nata domin ta samu cimma burinta kwarai da gaske .
Ita a na ta jawabin, babbar wakiliyar UNICEF’ofishin Jihar Bauchi , Bauchi, Mrs Nuzat Rafik,ta bayyana shi tsarin na TaRL,a matsayin daya daga cikin dabarar samar da ilimi a duniya.
Shi yasa ta ce duk kowa daga ciki al’umma yana da irin gudunmawar da zai bada wajen tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar da zai tafi makaranta, ta kuma kara jaddada tsarin nastressing TaRL yana bada dama ga Jihohi su samu kira da sa duk masu ruwa da tsaki.
A tasu gabatarwar ta hadin gwiwa, Dakta Goni Shetima,wanda shi horarwa ne ta bangaren tsarin TaRL,da Malam Abdulrahman Ibrahim Ado, kwararre jami’in ilimi na UNICEF, sun bayyana cewa tsarin an fara gudanar da shi a karamar hukumar Alkaleri.
Kamar yadda suka ce, an fara tsarin ne da makarantu 190, ‘yan makaranta 10,865, sai kuma Malaman makarantar gwamnati 290.
Shi ma darektan shiyya na hukumar (UBEC), wanda Abdulsalam Abubakar ya wakilta,ya bayyana irin jajircewar hukumar kan aiki tare da masu ruwa da tsaki, domin a samu bunkasa ilimi a fadin Jihar.
A nasu sa albarkar Shugaban kwamitin ilimi na majalisar Jihar, Honorabul Nasiru Ahmed Ala, darekta a SUBEB, Zuhairu Usman, da kuma darekata ingancin lamura SUBEB, Abbas Abdulmumini, sun yi kira da adauki tsauraran matakai wajen daukar Malaman makaranta, a daidai lokacin da gwamnatin Jihar ta ke shirin daukar Malaman makaranta.
A na shi fatan alkhairin Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu, wanda Danejin Bauchi, Alhaji Lawal Babamaji ya wakilta,ya bayyana Sarakunan gargajiya shirye suke wajen bunkasa ilimi a Jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp