Hukumomin Sadarwa a Nijeriya sun ce, sun dakile yunkurin kutse ko hare-hare a kan hanyoyin sadarwa na intanet har kimanin miliyan 13 a lokacin zaben shugaban kasa da aka gudanar a 25 ga Fabrairun 2023.
Babban daraktan hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta Nijeriya, NITDA, Kashifu Inuwa Abdullah, shi ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da BBC, inda ya ce an samu nasarar ce sakamakon wasu cibiyoyi da aka kafa don yaki da kutsen ta intanet da kuma wani kwamiti na musamman da aka kafa da ya kunshi hukumomin NITDA da NCC da Galaxy Backbone.
Ya ce a ranar zabe kadai sun dakile yunkurin kutse har miliyan shida da dubu dari tara.
Daraktan na NITDA ya ce an yi kokarin yin kutsen daga cikin gida da kuma ƙasashen waje saboda suna amfani da wasu manhajoji.
Ya ce kutsen ya shafi shafukan intanet na hukumomi da na kamfanoni masu zaman kansu da kuma na hukumar zabe wanda shi ne aka fi kai wa hari saboda zabe.