Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya ce, a ‘yan shekarun baya bayan nan, kasar Amurka ta dade tana tunzura kasar Philippines, da nufin ba ta kwarin gwiwar keta ikon mulkin kasar Sin a tekun kudancin Sin, don cimma makasudinta na siyasa. Hukuncin da aka yanke game da tekun kudancin Sin, ya saba wa yarjejeniyar dokokin teku ta MDD, tamkar dai wani wasa na siyasa, wannan ba shi da inganci ko amfani.
Lin Jian ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na yau da kullum, wanda ya gudana a yau Litinin, lokacin da wani dan jarida ya yi tambaya game da yanayin tekun kudancin Sin.
Lin Jian ya kuma gabatar da bayanai game da shawarwari don gane da harkokin tsaro bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha karo na 19, wanda za a yi gobe Talata, inda ya ce, Sin da Rasha za su zurfafa tattaunawa, da daidaita matsayinsu kan manyan batutuwan da suka shafi dangantakar bangarorin biyu, da tsaron kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, ta yadda za a kara amincewa juna tsakanin su. (Safiyah Ma)