Dangane da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano za ta yanke, kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, CP Muhammad Usaini Gumel, FIPMA, tare da sauran shugabannin hukumomin tsaro da ke aiki a jihar, sun tura isassun jami’ai da kayan aiki don jan kunne ga ‘yan siyasa masu yunkurin tayar da hargitsi.
An tura jami’an ne a wurare masu mahimmanci a cikin jihar don tabbatar da tsaro na rayuka da dukiyoyi da kuma dakile duk wani yunkuri na haifar da hargitsi ko rashin bin doka da oda.
- Kungiyar Kwadago Ta Tsunduma Yajin Aiki Yau Talata
- Ba Da Gudummawar Da Ta Dace Don Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Sin Da Afirka
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da jami’in hulda Jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba, 2023.
CP Gumel ya kara nanata cewa, rundunar ‘yansanda tare da sauran jami’an tsaro a jihar ba za su daga kafa ba ga duk wani da ke kokarin kawo cikas ga tsarin tsaro ba, don haka ake kira ga mazauna jihar, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali.