A halin da ake ciki kuma, tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ya nuna farin cikinsa da hukuncin kotun wanda ya tabbatar da nasarar APC Da Tinubu da Mataimakinsa Kashin Shettima, yana mai bayyana cewa dimokuradiyya ce ta yi nasara.
Ya ce Kotun ta kafa tarihi bisa yadda ta yi watsi da barazana da ce-ce-ku-cen da aka yi ta yi mata game da kararrakin zaben na shugaban kasa tare da yanke hukunci bisa doka kan zabin da ‘yan kasa suka yi.
“Idan akwai wanda ya yi nasara ma a yau, to demokuradiyya ce da kuma ‘Yan Nijeriya,” yana mai karawa da cewa, “bisa hukuncin da kotun ta yanke, yanzu magana ta kare, lokaci ne da za a manta da duk wasu abubuwa da suka faru a baya.
“Daga nan, ya kamata gwamnatin APC bisa jagorancin Asiwaju Bola Tinubu ta nemi goyon bayan kowa da kowa domin ta samu damar cika alkawuran da ta yi wa jama’a.” In ji shi.
Har ila yau, tsohon shugaban kasar ya yi godiya ga dukkan ‘yan kasa bisa zaman lumana da suka nuna a wa’adin mulkinsa tare da addu’ar kara samun ci gaba mai dorewa a karkashin gwamnatin APC.
Ya aike da sakon taya murna ga shugaban kasa da mataimakinsa da kuma Jam’iyyar APC bisa samun nasarar da suka yi a kotu tare da yi musu fatan cimma muradun al’umma.