Abokaina, shin kuna kallon gasar cin kofin kasashen Afirka ta AFCON dake gudana a kasar Kodibwa? Gaskiya yadda tawagar Najeriya ta doke Kodibwa a wasan da suka buga ranar Alhamis da ta gabata ya burge ni sosai. Inda kwallon da Ekong ya ci a bugun daga kai sai mai tsaron gida ya faranta mana rai. Kana wannan nasarar da kungiyar Najeriya ta samu ta sa nake fatan ganin ta sake yin nasara, a wasan da za ta buga da Guinea Bissau a ranar Talata mai zuwa.
Ganin kungiyar da nake goyon baya ta samu nasara, wani abu ne dake faranta rai matuka, sai dai wani abu da ya fi sa ni murna shi ne ganin yadda kasar Sin ke taka muhimmiyar rawa a fannin taimakawa gudanar da gasar AFCON. Ko kun san cewa, babban filin wasan da kungiyoyin Najeriya da Kodibwa suka yi wasa, wani kamfanin kasar Sin ne ya gina shi?
- Rikicin Wajen Aiki: Mutum Daya Ya Mutu, An Kama Mutum 14 A Kano
- An Cafke Mutumin Da Ya Kitsa Labarin Sace Kansa Don Karɓar Kuɗin Fansa Wurin Ɗan’uwansa
A kwanakin baya, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kammala ziyararsa a nahiyar Afirka, wadda ta kasance al’adar ministocin wajen Sin a farkon duk wata shekara. Kana yayin da yake ziyara a kasar Kodibwa, wadda take karbar bakuncin gasar AFCON na wannan karo, ministan wajen kasar Kacou Adom ya mika godiya ta musamman ga kasar Sin, inda ya ce, “Bisa taimakon da kasar Sin ta bayar, an mika manyan filayen wasa guda 3 cikin lokaci, kana wasu manyan motoci na bas masu yin amfani da wutar lantarki guda 6 da kasar Sin ta samar da su kyauta su ma sun iso Kodibwa. Ta haka, kasar Sin ta samar da muhimmiyar gudunmowa ga yunkurin kasar Kodibwa na karbar bakuncin gasar AFCON cikin nasara.”
Haka kuma a sauran wasu fannoni masu alaka da gasar AFCON ma, ana iya ganin gudunmowar da Sinawa suka bayar. Misali, dalilin da ya sa mutane a dimbin kauyukan kasar Najeriya samun damar kallon gasar AFCON, shi ne domin wani aikin tallafi da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa a kasashen Afirka, inda take samar da na’urar kama shirye-shiryen telabijin ta tauraron dan-Adam kyauta a kauyuka daban daban. Zuwa watan Disamban shekarar 2023, an kammala wannan aiki a kasashe 20 dake nahiyar Afirka, inda aka samar da hidimomi ga kauyuka 9512, shirin da ya amfani magidanta fiye da dubu 190. Ban da haka, dimbin kamfanonin kasar Sin sun shiga ayyukan watsa shirye-shirye masu alaka da gasar AFCON, da ba da tallafi ga wasu fannonin gasar, gami da taimakawa kasashen Afirka raya bangaren wasan kwallon kafa, da dai sauransu.
Me ya sa Sinawa ke dora muhimmanci kan gasar AFCON? Saboda sun san hadin gwiwar da ake yi mai alaka da gasar AFCON, za ta haifar da alfanu ga jama’a. Saboda jama’ar kasashen Afirka suna son wasan kwallon kafa, inda suke mai da hankali kan gasar AFCON, don haka taimakawa wajen ganin an gudanar gasar AFCON, tamkar biyan bukatar jama’ar kasashen Afirka ne, abin da ya haifar wa hadin gwiwar da ake yi a wannan fanni da ma’ana. Wannan ra’ayi ya samo asali ne a tunanin Sinawa na “mai da moriyar jama’a gaban kome”, kuma ya dace da babbar ka’idar Sin ta hadin gwiwa da kasashen Afirka, ta “gaskiya, da kauna, da sahihanci, gami da samar da hakikanin sakamako”.
A ganin Sinawa, huldar hadin kai da za ta amfani jama’a, hulda ce mai ma’ana. Sabanin haka, wasu kasashe sun dade suna fakewa da hadin gwiwa suna tilastawa kasashen Afirka amfani da wasu tsare-tsare na mulki da tattalin arziki, da sunan nagartaccen tsari, amma ba a taba samarwa jama’ar kasashen Afirka da zaman lafiya, da ci gaba, da jin dadin rayuwa ba, face tashin hankali da talauci.
Maimakon maganganu marasa dacewa da tsoma baki cikin harkokin gida na kasashen Afirka, kamata ya yi a gudanar da hadin kai, wanda zai samar da hakikanin sakamako da zai amfani jama’ar kasashen Afirka. Wannan shi ne tunanin da ya haifar da hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da Sin, dake zama wata halayyar musamman, wadda ta sha bamban da sauran hadin gwiwa. (Bello Wang)