Shugaban hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE), Farfesa Idris Bugaje, ya jaddada cewa ilimin fasaha da koyon sana’a sune manyan abubuwan da za su kawo ci gaba.
Bugaje ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi na bude taron kwana biyu na masu ruwa da tsaki a Kano kan tsarin lamarin ingantaccen ilimi domin bunkasar Afirka (BEAR III) aikin (2023 zuwa 2027), wanda hukumar kula da ilimi, kimiyya, da kuma al’adu dake karkashin majalisar dinkin duniya (UNESCO) tare da taimakon gwamnatin Korea.
- Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
- ’Yansanda Sun Kama ‘Yan Fashi A Kaduna, Sun Ƙwato Bindiga Da Wayoyi
Mataimakin darekta bangaren fasaha Dakta Babangida Ali- baba shi ne ya wakilin Farfesa Bugaje, ya bayyana muhimmancin ilimin fasaha a ci gaban tattalin arziki.
“Hanya kawai da zamu fitar da kasarmu daga kangin talauci shi ne tabbatar da cewar ilimi ana bashi kulawar data kamata, ta bangaren tattalin arziki, ”kamar yadda shi Shugaban NBTE ya bayyana, inda yake kara jaddada aniyar Shugabancin kan maida hankali wajen samar da dabaru na koyon yin abubuwa da suka hada da sana’oi da bullo da wasu, lamurran da zasu taimaka.
Ya yi karin bayani na hukumar NBTE ta kasance a gaba wajen bangaren samar da dabaru ta hanyar koyar da su,a makarantun fasaha afadin tarayyar Nijeriya, da zummar sa yadda za a koya masu abin ya zama da sauki.
A jawabinsa na maraba da mahalarta taron, Shugaba kuma Wakilin ofishin hukuma da ke Abuja wanda har ila yau wakilin UNESCO, na Nijeriya, Mista Mendy Albert, wanda Misa Manish Joshi ya wakilta, ya ce tsarin da akwai kwas na mako 10- ta kafar sadarwa ta zamani wanda aka kammala a watan Yuli, an shirya shi ne domin a karawa masu halartar taron yadda za su bunkasa da zamantar da ilimin koyon sana’a da fasaha.
Yace TBET wata babbar madafa ce da zata iya taimakawa matasa wajen koya masu dabarun da suka dace, wadanda ta haka ne za su damar tsayawa da kafafunsu dpomin samun bunkasar zamantakewa da tattalin arziki.
A nata jawabin,darekta ta fasaha da kimiyya ma’aikatar ilimi ta tarayya, Dakta Muhibat Adeleke Olodo, ta bada rahoton cewar fiye mutane milyan daya ne suka yi rajista da sabon tsarin TBET, da Kwalejojin gwamnatin tarayya suke maraba da dalibai 15,000 wannan watan.
Tace gyare- gyaren da ake son kawowa da niyyar samar da hanyoyin ayyuka, da kuma yadda za’a lura da bukatan masu saye domin yin amfani da abubuwan da aka yi ta amfani da ilimin fasaha, da samar da ayyuka ga matasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp