Uwargida na san tun da an ambaci kalmar tukunya to ba sai an yi bayani mai hakan ke nufi ba, an san kalmar sarrafa tukunya ita ake nufi da iya girki. Da yawa mata na fuskantar kalubale a gidan mazajensu saboda wannan matsalar, wanda idan aka yi la’akari za a ga cewa fa wannan babbar damuwa ce ga rayuwar aure musamman ga ‘ya mace, koda shima namiji za a so ya kasance ya san wasu daga ciki nau’o’i na girki ko don bacin rana.
Idan aka ce iya girki, ba fa ana nufin uwargida ta iya dafa taliya da indomi ba, sam ba haka bane irin wannan mace sai a ce mata ta rako.
- Yadda Uwargida Za Ta Yi Madarar ‘Soya milk’
- …Ya Kashe Uwargidan Da Yake Yi Wa Hidima Da Mahaifiyarta Gami Da Tafka Sata
Uwargida ya kamata ta san cewa namiji kamar jariri yake ta fannin cikinsa, idan kika kasance hannunki yana da zaki to fa akwai wani girma da kima na musamman da zai baki saboda kokarin da kika yi wajen kare masa yunwar cikinsa.
Bari mu koma baya mu gani daga ina matsalar take?
Iyaye mata a wannan fannin su ne, ke da kaso mafi tsoka na faruwa a irin wannan lamari, dalili kuwa shi ne sai ka ga yarinya ta tashi da safe ko tsintsiya ba za ta daga ba balle kuma a kai kan uwa uba hura wuta ta dora girki, yarinya kawai in ta tashi ta yi wanka ta yi shiri ta tafi makaranta zuwa da rana ta dawo ta samu abinci ya sauka ba ruwan uwar, ba za ta ce mata zo ki yi abu kaza ba sai dai kawai a barta zuwa yamma ta tafi islamiyya. Bayan kwana kadan a fara shela ai wance ta sauke Alkur’ani ai wance ta hada kwalin Digiri, amma inka bata tukunya ka ce sarrafa min abinci kaza to fa a nan ne ido zai raina fata.
Sai kuma a dawo ana biyan kudi ana tafiya makarantar koyon dafa abinci. Ya kamata iyaye su sani cewa girki shi ne mace, macen da ba ta iya girki ba ita da baho marabar su rai, saboda ba ta da amfani, babu wani amfani da za ta yi wa mijin.
Ya kamata mata su sani cewa, duk kyan mace in bata iya sarrafa abinci ba wannan kyan nata ya tashi a banza, ya kamata mace duk yadda take kuma a duk halin da ta tsinci kanta ta iya sarrafa abinci zuwa wani sabon launi. Akwai yanayi na rayuwa sannan kuma akwai sauyin rayuwa idan mace ta kasance ko da Mai da Barkono aka bata aka ce ta hada abinci, to ya dace a ce tana da iyawar da za ta iya sarrafa wannan kayan hadi a cikin abinci su ba da dandano mai gansarwa.
Akwai matan da mijinsu in dai zai ci abinci mai ma’ana to sai dai ya je gidansu ko kuma ya je gidan aboki saboda ita matar dai ta iya shafa hoda da jambaki amma ba za ta iya tuka tuwo a yi dumame ba, saboda tsabar rashin iyawa da safe sai dai a zubar ya zama ruwa. Ko kuma a yi girki zuwa dare ya jike ko kuma a dafa wake danye kuma kullum a haka ake tafia ba chanji.
Akwai matar da daga ruwan zafi babu abin da za ta iya sarrafawa, ko kuma ka ga mace har mace amma wai ita ba za ta yi tukin tuwo ba saboda gayu saboda hannunta zai lalace, ko daka sakwara to in ba ki yi wa mijinki ba a ina uwargida take so mijinta ya dinga cin abinci.
Amma idan mace ta iya wanka ta iya kwalliya, mu’amular aure sannan uwa uba ta iya girki to wannan mata ta kere sa’a sai dai a dinga gulma ana cewa ta mallake shi, amma mace ba kintsi tukunya ma babu dadi sannan kuma kina so miji ya soki, tabbas wannan babu gaskia a cikin sa.
Rashin iya girki ga mace babbar illa ce ga rayuwar da namiji saboda sai ciki ya koshi kwakwalwa ke iya sarrafa tunani, haka kuma iya girki na sa miji ya samu cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali, sannan kuma yana kara wa mace kima da daraja, to uwargida in kina gaza sauke hakkin cikinki ta ya za ki sami duk wadannan kulawar, sai ki ga kawai kina zama ne amma zaman ba wani armashi.
Akwai wata dabi’a da mata suka koya sai ka je gida ka tarar da mace wai sun karya da safe to fa shike nan an gama dafa abinci kuma sai da dare haka za a yi ta kame-kame ko kuma a ci kayan kwadayi, amma ba za ta iya zagewa ta dafa abinci ba. Wanan sam ba dabi’a ma kyau bace.