Wata sanarwa da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar Talatar nan 7 ga watan Nuwamba ta bayyana cewa, an yi hasashen samun karuwar GDPn kasar Sin da kashi 5.4 bisa dari a shekarar 2023.
Sanarwar da mataimakin darektan farko na asusun Gita Gopinath ya fitar, bayan wata ziyara da ya kai kasar Sin, ta bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana kan hanyar da za ta kai ga cimma burin gwamnatin kasar, na samun bunkasuwa a shekarar 2023, wanda ke nuna kyakkyawar murmurewa bayan annobar COVID-19. (Mai fassara: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp