Asusun bada lamuni na duniya IMF, ya yi hasashen tattalin arzikin kasar Sin zai karu zuwa kaso 5.2 cikin dari a bana, wato karuwar kaso 0.8 sama da hasashen da aka yi a watan Oktoban 2022.
Wannan na kunshe ne cikin sabon rahotonsa na hasashen tattalin arzikin duniya, da aka fitar jiya Litinin.
Rahoton ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin duniya zai fado daga kimanin kaso 3.4 a 2022, zuwa kaso 2.9 a 2023, sannan kuma ya karu zuwa kaso 3.1 a shekarar 2024.
Har ila yau, rahoton na sa ran hauhawar farashin kayayyaki zai fado daga kaso 8.8 a 2022 zuwa kaso 6.2 a bana, sannan ya kara sauka zuwa kaso 4.3 a 2024. Sai dai har zuwa lokacin, adadin hauhawar farashin ya dara kaso 3.5 da aka samu kafin barkewar annobar COVID-19. (Fa’iza Mustapha)