Kyaftin ɗin Argentina, Lionel Messi, ya ce yana fatan zai buga Gasar Kofin Duniya ta shekara ta 2026.
Sai dai ya bayyana cewa zai duba lafiyarsa kafin ya yanke shawara kafin zuwa gasar.
- Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100
- Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu
Messi, wanda yake taka leda a Inter Miami kuma yake da shekaru 38, ya jagoranci Argentina wajen lashe Kofin Duniya a 2022, kuma yana son sake wakiltar ƙasarsa yayin da za su kare kambunsu a Amurka ta Arewa a shekara mai zuwa.
A wata hira da NBC News, Messi ya ce: “Ina fatan na je gasar, amma duk zai dogara da yadda jikina zai kasance a wancan lokaci. Idan na kasance cikin ƙoshin lafiya, ina son na taimaka wa
ƙasata.”
Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, zai cika shekaru 39 a watan Yuni mai zuwa.
Ya ce yana jin daɗin zama a Miami bayan shekaru masu yawa da ya shafe a Barcelona da kuma lokacin da ya yi a Paris Saint-Germain.
Messi ya buga wasanni 195 tare da Argentina, inda ya zura ƙwallaye 114, kuma ya taimaka musu wajen lashe manyan kofuna kamar Copa América, Finalissima, da Kofin Duniya na 2022 a Qatar.














