Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce yana sane da mawuyaciyar tsadar rayuwa da ‘yan Nijeriya ke ciki biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi.
Shugaba Tinubu, ya ce ya yi fatan ace akwai wata dabara ko hanya da zai bi wacce za ta farfado da tattalin arzikin Nijeriya ba tare da cire tallafin man fetur ba amma babu.
Tinubu, wanda ya bayyana hakan a yayin wani jawabi da ya yi a fadin Nijeriya a yammacin ranar Litinin, ya ce, bai cire tallafin ba da nufin cutar da masu kananan karfi ba , amma ana bin duk hanyoyin da suka kamata don lalubo matakan rage radadin cire tallafin.
Cikakkun bayanai na nan tafe…