Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu. Akramakallah tambaya gare ni kan wani ruwa ke fitomin amma kuma ba jini ba ne. Ina ganin sa kasa-kasa, babu wari ko karni tare dashi.
Ina ganin sa idan na yi Azumi ko na yi aiki sosai sai marata ta yi ciwo yake fito min. Yaya Azumina da sallata take shin zan cigaba da yin su? Sannan yana fitomin wajan karfe 3 na rana ne.
Wa’alaikum assalam, mutukar ba jini ba ne, kuma ba baki ba ne, ba shi da karni, to ba zai hana sallah da azumi ba, zai yi kyau ki je wajan likita don ya duba lafiyarki, saboda abin da kika gani zai zama ba jinin haila ba ne, tun da ya rasa daya daga cikin siffofinsa. Allah ne mafi sani.