Gwaman jihar Binuwe, Samuel Ortom ya bayyana cewa, ya na sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kawai sabida ya gaza kawo karshen kashe-kashen da ‘yan Bindiga ke yiwa al’ummar jiharsa.
Gwamnan wanda ya mayar da matarni kan jinjinawar da shugaban kwamitin Majalisar wakilai kan harkokin ilimin manyan makarantun, Aminu Suleiman Goro ya yi wa Shugaban kasa.
Goro ya kaddamar da wasu ayyukan more rayuwa da gwamnatin Buhari ta yi a ma’aikatar koyon aikin noma dake Makurdi babban birnin jihar, Goro ya nemi gwamna Ortum da ya dinga yin dubi da irin kokarin da Gwamnatin Buhari ke yi wajen yin ayyuka a jiharsa, Binuwe.
Gwamna Ortom, a wani jawabin da ya gabatar a cocin Faith Cathedral, ya ce, ba zai daina sukar gwamnatin Buhari ba har sai an yi maganin ‘yan bindiga, inda ya ce, da Gwamnatin Tarayya ta dauki shawarar sa, da yanzu ba a zo a inda ake ba.
Ya ce, a 2016 ya fara yin magana a kan kalubalen na rashin tsaro, amma mai makon a dauki shawarar sa, sai aka koma yi masa bita da kulli, inda ya ce, ga shi a yanzu kalubalen ya ba zu zuwa wasu jihohin kasar nan.