Hukumar zaben mai zaman kata ta kasa reshen Jihar Zamfara ta ba wa zababben gwamnan Jihar Zamfara na Jamiyyar PDP, Dr Dauda Lawal Dare, takardar shaidar nasarar cin zaben gwamnan Jihar a ayu Juma’a.
Shugaban Hukumar Zabe reshen Jihar Zamfara, Farfesa Saidu Babura, ne ya jagoranci bikin mika takardar lashe zaben ga dan takarar da ya samu nasara a zaben da ya gabata.
Yanzu haka Dr. Dauda Lawal Dare, shi ne zabebben gwmana mai jiran kama rantsuwar aiki nan da 29, ga watan Mayun 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp