Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta nuna matukar damuwarta game da rashin amsar katunan zabe har guda 360,000 a Jihar Kano.
Kwamishinan zabe Jihar Kano, Ambasada Abdu Zango, shi ya sanar da hakan a ranar Asabar lokacin da ya karbi mambobin kwamitin da gwamnan Jihar Kano ya kafa don kara wayar da kan jama’a game da sabon rajistar masu kada kuri’a da ake gudanarwa a yanzu.
- Sin: Shawarar Gina Kyakkyawar Makomar Bil Adam Ta Bai Daya Ta Samu Amincewa A Duniya
- Yadda Aka Gudanar Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya A Kano
Kwamitin da ke karkashin shugabancin kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamade Ibrahim Abdullahi Waiya, ana sa ran zai wayar da kan masu kada kuri’a kan muhimmancin karbar katin zabensu da kuma shiga cikakken harkokin jefa kuri’a a lokacin zabe.
Ambasada Zango ya ja hankali kwamitin da ya kara zage damtse wajen yin gaggami, yana mai cewa dukkan katunan da ba a amsaba har yanzu suna hannun INEC.
Ya yaba wa gwamnatin jihar da ta kafa wannan kwamiti, yana mai cewa mambobin kungiyar da shugabanin Waiya za su taimaka wajen gudanar da wannan aiki cikin nasara.
Ya kuma tabbatar da cewa kwamitin zai hadin kai da INEC wajen wayar da kan masu zabe kan sabon rajistar da kuma amsar katunan zaben.
Da yake magana a fadar gidan gwamnatin Jihar Kano, kwamishinan yada labaran ya bayyana cewa Gwamnan Jihr Kano, Abba Kabir Yusuf ne da kansa ya kafa kwamitin don shigar da dukkan kungiyoyi a cikin jihar, ciki har da jam’iyyun adawa, domin karfafa shigar kowa cikin harkokin zabe.
Ya bukaci INEC da duba yuwuwar karin adadin wuraren jefa kuri’a a Kano don saukaka cunkoso a lokacin gudanar da zabe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp