Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta cire sunan Alhassan Ado Doguwa daga jerin ‘yan majalisar wakilai da suka lashe zaben ranar 25 ga watan Fabirairu 2023.
Dogowa wanda shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai kuma mai wakiltar mazabar Doguwa, Tudun Wada a Jihar Kano, jami’in zabe na INEC Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ne ya sanar da sunan Dogowa a matsayin wanda ya lashe zaben a jam’iyyar APC, inda ya samu kuri’u 39,732 ya kuma doke abokin takararsa na jam’iyyar NNPP, Yushau Salisu Abdullahi wanda ya samu kuri’u 34,798.
- Ba Za Mu Bari NNPP Ta Yi Magudin Zabe A Kano Ba —Gwamnatin Kano
- Jam’iyyar NNPP Ta Bukaci Jami’an Tsaro Su Tabbatar An Yi Sahihin Zabe A Kano
A sabon sunayen zababbun ‘yan majalisar wakilai da INEC ta fitar, ya nuna babu sunan Doguwa a ciki.
A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda Farfesan muryarsa ke rawa a lokacin da yake sanar da sakamakon zaben.
An ruwaito cewa, rikici dai ya barke a mazabar ta Doguwa bayan an kammala zaben, inda hakan ya sa jami’in tsaro suka kama Doguwa bisa zarginsa da hannu wajen kashe mutane da kone sakatariyar NNPP
Amma Doguwa ya karyata zargin.
An dai gurfanar da Doguwa a gaban kotu, inda kotun ta tuhume shi da kisa da tayar da yamutsi ta kuma tura shi ajiya a gidan gyaran hali
Sai dai, kotun tarayya da ke da zamanta a Kano, ta bayar da belin Doguwa a kan kudi Naira miliyan 500 ta kuma haramta masa zuwa mazabarsa a ranar zaben gwamnoni da ke tafe.