Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bukaci ‘yan jarida da kafafen watsa labarai da su kaurace wa gaggawar yada labarai, wato labarai da duminsu, tsaurara kanun labarai domin jawo hankalin masu karatu gami da karkarar da labarai don kauce wa rurutawa gami da zafafan lamuran zaben.
Babban kwamishina kuma shugaban sashen yada labarai da ilmantar da masu zabe na INEC, Barista Festus Okoye, shi ne ya yi wannan kiran a yayin wani taron kara wa juna sani na wuni guda da kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) ta shirya kan rahotonni masu tada hankali a yayin zaben 2023.
- Kotu Ta Wanke Babachir Lawal Daga Zargin Damfarar N544m
- Jerin ‘Yan Wasan Da Kasashe Suka Gayyata Zuwa Kofin Duniya
Okoye da ke samun wakilcin mataimakin daraktan hulda da jama’a na hukumar, Misis Chinwe Ogbuka, ya ce, wasu gidajen jaridun sun hummatu wajen rige-rigen fitar da labarai ta hanyar shafukansu na yanar gizo wanda a irin hakan wasu lokutan ma su na yada labarai da basu da sahihanci balle inganci.
Ya ce, a wasu lokutan da gangan wasu kafafen ke amfani da tsauraran kanun labarai kawai don su samu kasuwa ta hanyar yawan masu ziyartar shafukansu.
Shi kuma Shugaban ‘yan jarida ta kasa Mr Chris Ishiguzo, ya nuna damuwar cewa wasu ‘yan jarida da dama sun rasa rayukansu a lokacin da suke bakunan aikinsu wasu kuma sun gamu da munanan raunuka, a yayin da wasu kuma kayan ayyukansu suka lalace musamman a lokuktan zabuka.
Kan hakan ya bukaci masu ruwa da tsaki da su daina amfani da ‘yan bangar siyasa domin tabbatar da kariya da lafiyar masu gudanar da ayyukansu.
Shugaban ya ce akwai bukatar kare rayuka da lafiyar ‘yan jarida domin su samu zarafin gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.