INEC ta tabbatar da kama wani jami’in tsaro da ke yin aiki a ofishinta da ke a karamar hukumar Obio Akpor ta jihar Ribas, bisa zargin karbar cin hanci daga wurin jama’a don yi masu rijistar katin zabe.
Kakakin hukumar ta INEC da ke jihar, Geraldine Ekelemu, ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a jihar.
Ya bayyana cewa, jami’an ‘tsaron farin kaya ne suka cafke jami’in.
- Dalilinmu Na Karbar Sunan Ahmed Lawan Maimakon Na Machina – INEC
- Adamu Yaki Cewa Uffan Kan Mika Sunan Lawan Da Akpabio Ga INEC
Sanarwar ta kara da cewa, hukumar ba za yarda ta bari ana karbar cin hanci domin a yi wa jama’a rijistar katin jefa kuri’ar ba.
Sanarwar ta kuma bayar da tabbacin cewa jami’an tsaro za su gudabar da cikakken bincike kan zargin amasar na Goro da wasu Jami’an hukumar ke yi tare da hukuntasu kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Dubun jami’in dai ta cika ne biyo bayan yawan zarge-zargen Jama’ar yankin kan cewa wasu Jami’an hukumar na karbar toshiyar baki daga gun mutanen da ke karamar hukumar ta Obio Akpor kafin su yi masu rijistar zaben.
A kashe, sanarwar ta bukaci jama’a da su kai rahoton Jami’an hukumar da ke karbar cin hanci daga wurin jama’a don su yi masu rijista.