Gwamnan jihar Ekiti, Mista Biodun Oyebanji ya sanar da sauye-sauye a majalisar zartarwa ta jihar nan take biyo bayan sallamar kwamishinoninsa 19.
Sallamar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar, Farfesa Habibat Adubiaro ta sanya wa hannu, kuma ta mika wa manema labarai a yammacin jiya Lahadi.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15
- Ofishin Jakadancin Sin A Birtaniya Ya Soki Furucin Kasashen G7 Dangane Da Yankin HK
Kwamishinonin da abin ya shafa da masu ba su shawara na musamman a cewar sanarwar, an umurce su da su mika ragamar ofishinsu ga babban sakatare ko babban ma’aikacin gwamnati a hukumominsu.
Gwamna Oyebanji ya godewa ‘yan majalisar zartarwar jihar da abin ya shafa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.
Sai dai, umarnin bai shafi babban Lauyan jihar da kwamishinan shari’a ba.
Har ila yau, daga cikin wadanda sallamar ba ta shafa ba, akwai Kwamishinonin Lafiya da Ayyukan Jama’a, Noma da Tattalin Abinci da Ayyuka.
Bugu da kari, kwamishinan ciniki, saka hannun jari, masana’antu da kungiyoyin hadin gwiwa; Mai ba da shawara na musamman kan Ilimin masu bukata ta Musamman; da mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsaren kasa, duk suna nan kan mukamansu.
Haka kuma, duk Daraktocin da ke cikin majalisar zartarwa ta Jihar, za su ci gaba da rike mukamansu.