Gwamnatin Jihar Gombe a karkashin jagorancin Muhammadu Inuwa Yahaya, ta dauki sabbin Jami’an kiwon lafiya a kalla dari hudu da arba’in (440) a kokarinta na ingantawa da kyautata sashin kiwon lafiya a fadin jihar.
Sabbin ma’aikatan za a turasu zuwa kananan asibitocin kiwon lafiya da suke fadin jihar domin magancewa da shawo kan ‘yan matsaloli karancin ma’aikata da ake fama da su a asibitocin domin inganta aikin kiwon lafiya a matakin farko.
Da ya ke taya sabbin ma’aikatan murna, kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ya jawo hankalinsu da su maida hankali wajen gudanar da aiki tukuru domin sauke nauyin da ke kawukansu.
Ya yi bayanin cewa, gwamnati mai ci a jihar ta bada fifiko da muhimmanci ga sashin kiwon lafiyan jama’a.
A nasa bangaren, babban Sakataren hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar, Dakta Abdulrahman Shuaibu, ya jawo hankalin sabbin ma’aikatan da a kowani lokaci da suke bin ka’idoji da kwarewar aiki yayin da suke gudanar da ayyukansu.
Ya ce, Gwamnatin jihar jihar tun lokacin da ta dale karagar mulki ta baiwa sashin kiwon lafiya fifiko ta hanyar daukan ma’aikata, samar da kayan aiki, maguna, ginawa da kwaskwarima wa cibiyoyin lafiya a fadin jihar.